An dawo da martabar Kano — Sarki Sanusi II

Sarki ba ya fadanci ba ya kirara amma tabbas Gwamna Abba Kabir ya cika gwarzo.

An dawo da martabar Kano — Sarki Sanusi II

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf da Majalisar Dokokin Kano sun dawo da martabar tarihin Masarautar Dabo.

Sanusi II ya faɗi haka ne a yayin jawabin da ya gabatar bayan karɓar takardar kama aiki a matsayin Sarki Kano.

Sarkin ya ce rushe masarautun da aka ƙirƙiro tare da dawo da Kano ƙarƙashin masarauta ɗaya ya tabbatar da dawo da jihar kan turba da martaba da tarihin da aka santa a kai.

“Larabawa sun kasance suna faɗin cewa a duk abin da za mu shaida, akwai darasi da ke nuna mana cewa Allah Yana nan, duk abin da ke faruwa ga mutum Allah ne Ya riga Ya ƙaddara, kuma ga masu hankali, wannan darasi ne.

“Allah ɗaya ne kuma duk abin da Ya yi babu mai iya canzawa, abin da bai Yi ba kuma ba wanda zai iya.

“Kimanin shekaru 10 da suka gabata a wannan waje tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba ni takardar naɗa ni a matsayin Sarkin Kano, yau bayan kusan shekara 10 gani na sake karɓar takardar naɗin sarauta a hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce “da an bar batun rarraba masarautu a Kano, to da an ci gaba da rarraba masarautu a jihar kenan.

“Da an bar wannan lamari na rarraba masarautu to da wata rana sai an naɗa Sarkin Fagge, ko Kunci ko Kumbotso,” in ji shi.

“A Arewacin kasar nan, mun gani a jihohi daban-daban yadda ‘yan siyasa suka rusa martaba da tarihin masarautu, inda a jiha ɗaya sai a samu Sarki ɗaya ya zama 20, wasu 19.

“A jihohin Arewacin Najeriya, akwai ƙananan hukumomin da sai a samu sarakuna biyu ko uku.

“Lokaci ba zai ba ni damar yin wasu maganganu ba. Duk abin da za mu ce mun faɗi lokacin da za mu tafi.

“Mun bayyana cewa Allah Yana ƙaddara lokaci da dalili a kan komai da kowa. Ya ba da shugabanci ga wanda yake so kuma a lokacin da yake so. Idan ya bayar ba mai iya ƙwacewa, idan kuma Ya karɓa, babu mai iya bayarwa.

“Gwamna da ’yan majalisarmu ba za ku gane girman abin da kuka yi wa tarihin Kano da kasa baki ɗaya ba.

“A cikin Sarakunan Kano, an fara ne daga Bagauda sama da shekaru 1000 da suka gabata.

“Haka kuma a cikin tsawon wannan shekaru, an taɓa samun Sarki Muhammadu Koguna da aka tube masa rawani, ya dawo bayan wasu kwanaki.

“Wannan ya nuna cewa a cikin shekaru 1000, babu wani sabon abu dangane da lamarin da ya faru a yanzu.

Sarkin ya ce ’yan majalisa da gwamnatin sun ceto tarihi babba wanda yake haɗa kan al’umma.

Muhammad Sanusi II ya ce Sarki ba ya fadanci ba ya kirari amma yana faɗar gaskiya, yana mai cewa lalle gwamnan jihar ya cika gwarzo.

Sarkin ya kuma gode wa gwamna da al’ummar Kano.

Muhammadu Sanusi II ya ce babu wani wanda yake da wani gida a Masarautar Kano duk zuri’ar Dabo ɗaya ce wanda shi ne ya kafa Masarautar Kano.

Haka kuma, Sarkin ya ce ba zai tofa komai ba a kan waɗanda suka cire shi saboda a cewarsa ba su isa komai ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, a jiya Alhamis ce Gwamna Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

“Bayan soke dokar masarautu ta Jihar Kano ta 2019, hakan na nufin cewa masarautar Kano ta koma matsayinta gabanin dokar ta 2019”, a cewarsa jim kadan bayan sanya hannu kan sabuwar Dokar Masarautun Kano.

Ya ƙara de cewa “hakan na nufin babu wani halastaccen Sarki a Kano sai Sarki Muhammadu Sanusi.”

Da safiyar ranar Alhamis ce Majalisar Dokokin Kano ta yi wa Dokar Masarautun Kano ta shekarar 2019 garambawul, inda ta rushe duka masarautun jihar biyar.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro