An dawo da wutar lantarki a Kaduna
An dauke wutar ne sakamakon yajin aiki da ma’aikatansa suka shiga tsawon kwana biyar.
![An dawo da wutar lantarki a Kaduna An dawo da wutar lantarki a Kaduna](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/1738969166870.jpg)
A cikin daren nan aka dawo da wutar lantarki a Jihar Kaduna.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) ya dawo da wutar be bayan kwanaki babu ita.
An dauke wutar ne sakamakon yajin aiki da ma’aikatansa suka shiga tsawon kwana biyar.
Kaduna Electric ne ke ba da wutar lantarki a Jihar Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi.
Ma’aikaran sun janye yajin aikin ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya shiga tsakaninsu da kamfanin.