An dawo da zoben kammala makaranta bayan shekara 67 da bacewarsa
Shekarar zoben 67 da bacewa ke nan
Wani zoben kammala makaranta na wata daliba da ya bace shekara 67 da suka gabata ya koma ga ainihin mai shi.
Kafar labarai ta UPI, ta ruwaito a ranar 18 ga Janairun bana, cewa wata mata ’yar Jihar Texas da ke Amurka da ta mallaki zoben ta dauka ta jefar da zoben ne, amma an gano an sace shi ne, inda aka sanya shi a matsayin shaida a 1986 lokacin wata shari’a kan miyagun kwayoyi.
- ISWAP ta kori ’yan Boko Haram daga zama ’ya’yanta kan zargin zagon kasa
- INEC ta sake kara wa’adin karbar katin zabe
Babban Alkalin Gundumar Parker, Mista Jeff Swain ne ya gano zoben tare da wani zoben sojin sama a cikin wata ambulan da aka adana a ma’ajiyar kotun gundumar da ke ginin Weatherford a Texas.
Alamar P.W ce ta sa aka gano ainihin mai zoben wadda ta kammala makaranta a Dupo High School a 1956.
Swain ya kaddamar da bincike don gano mai zoben ta duba bayanan daliban da suka kammala makarantar a 1956 a Dupo High School da ke Jihar Illinois ta Amurka.
Ya gano daliba daya ce kadai ke da farkon suna mai alamar P.W, cewa wata mata mai suna Peggy Wall.
Swain ya nemi taimako daga mai bincike na gundumar, Mista Wendy Brabo, wanda ya yi kidayar 1950 don gano iyalan Misis Wall, shi kuma ya sanar da shi cewa Misis Wall tana zaune ne a garin Keller na Jihar Texas.
Bravo ya mika wa Wall zobenta, tare da zoben sojin sama wanda aka gano na tsohon mijinta ne.