An dawo wa dakin karatu littafin da aka ara shekara 63 da suka gabata
Da babu gara babu dadi! Ina neman afuwa kan makara wajen maidowa!
Wani dakin karatu a Ingila ya ce, an dawo masa da wani littafi ta gidan waya bayan daukar aronsa shekara 63 da suka gabata, hade da sakon “da babu gara ba dadi.”
Kafar labarai ta UPI ta ce dakin karatun a Newcastle Libraries ya sanya a shafinsa na Facebook yana nuna kwafin littafin Darrell Huff mai suna How to Lie with Statistics.
- Lalata da mata: ‘Gwamnan New York ya sauka kawai’
- Manyan shari’o’i 5 da aka ‘kwanta’ kansu a Najeriya
Bayanai sun ce littafin wamda aka maido ya iso ta gidan waya bayan an dauki aronsa daga dakin karatu na Central Library shekara 63 da suka gabata.
Jami’an dakin karatun sun ce, an hado littafin da wani sako mai cewa: “Da babu gara babu dadi! Ina neman afuwa kan makara wajen maidowa!”
Manajan dakin karatun Mista David Hepworth wanda ya dawo da littafin bai bayyana sunansa ba.
Ya shaida wa BBC cewa, “Kila sun damu kan kudin da za mu nemi su biya ne.”
Jami’ai sun ce ajiye littafin na tsawon lokaci zai iya jawo biyan tarar Dala 4,722.54 (kimanin Naira miliyan biyu da dubu 266 d 819).
Mista Hepworth ya ce mutumin ya rika zille wa kokarin karbo littafin a shekarun baya, bayan ya tafi da shi.
“A wadancan shekaru har zuwa shekarun 1970, akwai jami’in dakin karatu da yake ziyartar mutane a gidanjensu domin karbo littattafan,” inji Hepworth.
Ya ce, “A gaskiya yanzu ba ma yin haka.”
Mista Hepworth ya ce, yana fata mutumin da ya dawo da littafin zai fito ya nuna kansa.
Ya ce jami’an dakin karatun ba sa son karbar tara, maimakon haka suna so ne su saka wa mutumin da kyautar littattafan da kamfaninsu na Tyne Bridge ya wallafa.