An dibar wa Dolphins kwanaki 60 ta biya albashi ko a zaftare mata maki 6
Kwamitin ladabtarwa na hukumar kula da shirya gasar rukuni-rukuni na Najeriya (LMC) ya bukaci kulob din Dolphins da ke Fatakwal ya gaggauta biyan basussukan albashin da ’yan kwallonsa ke bi daga nan zuwa kwana 60 ko kuma ya fuskanci hukuncin hukumar. Hukumar ta ce muddin kulob din ya gaza biyan ’yan kwallon kafin wa’adin da […]
Kwamitin ladabtarwa na hukumar kula da shirya gasar rukuni-rukuni na Najeriya (LMC) ya bukaci kulob din Dolphins da ke Fatakwal ya gaggauta biyan basussukan albashin da ’yan kwallonsa ke bi daga nan zuwa kwana 60 ko kuma ya fuskanci hukuncin hukumar. Hukumar ta ce muddin kulob din ya gaza biyan ’yan kwallon kafin wa’adin da aka dibar masa to za a zaftare masa maki shida daga adadin makin da ya hada kawo yanzu a gasar firimiya sannan za a cigaba da zaftare masa maki uku-uku a kowane wata har sai ya biya ’yan kwallon.
Kulob din ya amince da hukuncin da aka dauka a kansa ne bayan ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwar da hukumar ta kafa bayan ya tabbatar da gaskiyar labarin.
daya daga cikin ’yan kwallon kulob din Emeka Atuloma ne ya fara shigar da kara daga bisani Hukumar LMC ta kafa kwamitin binciken da ya tabbatar da gaskiyar lamarin.
Bayan binciken ne kwamitin ya aika wa kulob din matakin da aka dauka akansa na dibar masa wa’adin kwanaki 60 da ya biya ’yan kwallon albashin da suke bi ko ya fuskanci hukuncin zaftare maki shida daga adadin makin da ya hada kawo yanzu a gasar rukuni-rukuni na Najeriya da aka fi sani da GLO Premier League da yanzu haka ake yi. Sannan za a cigaba da zaftare maki uku a kowane wata har a gama gasar muddin kulob din bai biya ’yan kwallon albashinsu ba bayan cikar wa’adin.
Rahotanni sun ce tuni kulob din ya fara yunkurin biyan ’yan kwallon don kauce wa fadawa tarkon hukumar.