An fadakar da ‘yan majalisar Bauchi kan matsalar abinci ga yara

Kungiyar fadakar da al’umma kan kiwon lafiya ta bangaren yada labarai ta kasa da kasa (ISMPH) da hadin gwiwar Kungiyar da ke bibiyar ayyukan ‘yan majalisan kasar, CISLAC da gidauniyar Aisha Buhari, ne suka shirya taron fadakarwa kan matsalar abinci mai gina jiki ga yara da aka yi wa ‘Yan Majalisar dokokin jihar Bauchi a […]

An fadakar da ‘yan majalisar Bauchi kan matsalar abinci ga yara

Abubakar Y Suleiman Shugaban Majalisar Dokokin jihar Bauchi

Kungiyar fadakar da al’umma kan kiwon lafiya ta bangaren yada labarai ta kasa da kasa (ISMPH) da hadin gwiwar Kungiyar da ke bibiyar ayyukan ‘yan majalisan kasar, CISLAC da gidauniyar Aisha Buhari, ne suka shirya taron fadakarwa kan matsalar abinci mai gina jiki ga yara da aka yi wa ‘Yan Majalisar dokokin jihar Bauchi a Gombe.

A lokacin taron da ya gudana a Gombe shugaban Majalisar tsara dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y Suleiman Dan Galadiman Ningi, ya bayyana cewa Majalisar zata kafa dokar ta baci kan matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar bayan fitowar wani rahoto na shekarar 2019 da ya nunar da mutuwar yara 94 ‘yan kasa da shekaru biyar.

Shugaban Majalisar, ya ce matsalar tamowa a jihar ya ta’azzara hakan ne yasa nan take ya yanke hukuncin cewa za su kafa dokar ta baci sannan kuma za suyi zama da ma’aikatar lafiya dan ganin yadda za’a shawo kan matsalar.

Ya kuma ce, ba gaskiya bane yadda ake ta yayata jita jitar cewar ‘Yan Majalisa ne suka cire kason kudi na yaki da rashin abinci mai gina jiki na (SAM) ‘Severe Acute Malnutrition’ a kasafin kudin da ya gabata.

Shugaban Majalisar ya godewa kungiyoyin da suka shirya musu wannan taron sai ya yi kira ga sauran kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba NGOs da su yi koyi da wadanann kungiyoyi.

Da yake zantawa da Aminiya, jami’in kula da harkar abinci mai gina jiki na jihar Bauchi Malam Abubakar Saleh, ya ce gaskiyar al’amari shi ne an samu mutuwar yara 94 a jihar, yayin da aka kwantar da yara sama da dubu 23 a shekarar da ta gabata.

A cewar Jami’in a shekarar ta 2019 kimanin yara dubu 23, 133 ne aka kwantar a cikin su ne aka samu kimanin dubu 22, 133 har guda 94 suka mutu .

Ya kara da cewa, kimanin rahotannin bullar cutar 311 ba a iya samun alkaluman su ba, inda guda 84 aka canja musu asibitoci zuwa manyan cibiyoyin kiwon lafiya saboda yanayin halin da suke ciki, wasu guda 1,266 basu iya samun kulawa ba.

Solomon Dogo jami’i a ISMPH a wajen taron

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos