An fara bajekoli a Kano
A ranar Asabar din makon jiya Cibiyar Bunkasa Ciniki da Masana’antu da Ma’adinai da Ayyukan Gona (KACCIMA) ta Jihar Kano ta bude bikin bajekoli na kasa a dandalin bajekoli da ke kan titin gidan namun daji a Kano. Bajekolin na bana wanda aka yi masa take da ‘inganta amfanin gona da habaka ayyukan masana’antu wanda […]

A ranar Asabar din makon jiya Cibiyar Bunkasa Ciniki da Masana’antu da Ma’adinai da Ayyukan Gona (KACCIMA) ta Jihar Kano ta bude bikin bajekoli na kasa a dandalin bajekoli da ke kan titin gidan namun daji a Kano.
Bajekolin na bana wanda aka yi masa take da ‘inganta amfanin gona da habaka ayyukan masana’antu wanda bai shafi man fetur ba’ shi ne karo na 35 da aka fara yin bajekoli a jihar.
Alhaji Safiyanu Baba shi ne mataimakin Shugaban kwamitin tsare-tsare na wannan baje-koli, a hirarsu da Aminiya ya bayyana cewa an tsara taken bajekolin na bana ne don samun mafita ga jama’a daga tunaninsu na dogaro da man fetur, kasancewar man fetur ba abu ne mai dorewa ba.
“Ta hanyar wannan bajekoli muna son samar wa mutane hanyoyin kasuwancin na daban, musamman wadanda suka shafi masasana’antu don inganta kasuwancinsu. Wannan shi zai dauke hankalin mutane daga dogaro da man fetur da ake yi. Idan mun duba shi kansa man fetur ba abu ne mai dorewa ba. Hakan ya sa muka gayyato masu ruwa da tsaki a harkar kamfanoni da masana’antu don su wayar wa jama’armu kai a kan sha’anin kasuwancin da ba na man fetur ba.” Inji shi.
Da yake jawabi game da kamfanonin da suka shiga wannan bajekoli Alhaji Safiyanu Baba ya bayyana cewa akwai kamfanoni masu yawan gaske da suka hada da na gida da kuma na kasashen ketare a filin wannan bajekoli.
“Muna sa rai bajekolin bana zai fi na bara armashi, domin daga ganin yadda abubuwa ke tafiya za a fahimci cewa za ta fi wacce aka yi a baya. Kasancewar kamfanoni masu yawa daga kasashen waje irin su China da Indiya da Turkiyya da Pakistan sun zo wurin wannan bajekoli. Ina ganin mutane za su samu damar kulla dangantakar kasuwanci da kamfanoni masu yawa, musamman wadanda ke da masana’antu, ta yadda za su tattuna game da yadda za su samu ci gaban sanao’insu.”
Shugaban ya yi kira ga jama’ar jihar da su yi amfani da wannan dama wajen fitowa don kulla dangantakar kasuwanci da kasashen waje, kasancewar jihar cibiya ce ta kasuwanci.
“Ya kamata jama’ar Jihar Kano su fahimci cewa domin su ake wannan bajekoli, duka wadannan mutane da muka gayyato mun gayyato su ne don mu ga cewa harkokin kasuwanci sun kara habaka a Kano. Dama Kano ita ce cibiyar kasuwanci ba ma a kasar nan ba, har ma a cikin kasashen Afirka. Haka a lokutan bajekoli ne mutum zai ga abubuwan da ba ya ganin su a kasuwa, kasancewar akwai baki, don haka muke kira ga jama’a su shigo wannan kasuwa don ganin abubuwan da ke akwai.” Inji shi.
A yanzu haka dai kamfanoni da kananan ’yan kasuwa sun fara baje hajarsu a rumfuna da aka tanada don wannan biki, sai dai akwai karancin fitowar jama’a zuwa filin bajekolin, lamarin da jama’a suka
bayyana da cewa hakan yana da alaka da yanayin matsin tattalin arziki da jama’ar kasar nan ke ciki, sannan akwai rashin samun albashi a hannun ma’aikata.