An fara bikin kawo karshen Ebola a Saliyo

A jiya Alhamis kasar Saliyo ta fara bukukuwa gabanin gobe Asabar da ake shirin ayyana kasar a matsayin wadda babu sauran wanda yake dauke da kwayar cutar Ebola, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.Kodayake, kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce kimanin kashi 80 cikin 100 na mutanen da suka warke […]

An fara bikin kawo karshen Ebola a Saliyo
An fara bikin kawo karshen Ebola a Saliyo

A jiya Alhamis kasar Saliyo ta fara bukukuwa gabanin gobe Asabar da ake shirin ayyana kasar a matsayin wadda babu sauran wanda yake dauke da kwayar cutar Ebola, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Kodayake, kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce kimanin kashi 80 cikin 100 na mutanen da suka warke daga cutar na fama da wasu matsaloli kamar ciwon gabobi da kuma kasalar jiki. Har ila yau, akwai wasu mutanen da suka warke, amma suka fama da makanta, sai dai masu bincike na kokarin gano dalilin hakan.
kungiyoyin mutanen da suka warke daga cutar sun ce babbar matsalar da suke fuskanta ita ce ta kyamar da ake nuna musu, da kuma jin damuwar cewa sun warke yayin da wasu suka mutu.
A farkon shekarar nan ne aka ruwaito cewa akalla yara dubu 12 ne cutar ta mayar marayu a kasar. Mutum 3,949 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar annobar  a kasar. Hakazalika,  fiye da mutum dubu 10 ne cutar ta yi ajali a kasashen Laberiya da Guinea da kuma Saliyo.