An fara bincike kan bai wa dan ISIS bizar shigowa Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a binciki yadda aka yi aka ba wani jagoran kungiyar ISIS bizar shigowa Najeriya a kasar Lebanon.Imam Ahmed Al-Assir, wanda aka yanke wa hukuncin kisa a bayan idonsa yana wasan buya da hukumomin kasashen duniya da dama tun shekarar 2013, kuma a ranar Juma’ar da ta gabata […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a binciki yadda aka yi aka ba wani jagoran kungiyar ISIS bizar shigowa Najeriya a kasar Lebanon.
Imam Ahmed Al-Assir, wanda aka yanke wa hukuncin kisa a bayan idonsa yana wasan buya da hukumomin kasashen duniya da dama tun shekarar 2013, kuma a ranar Juma’ar da ta gabata ne hukumomin tsaron Lebanon suka kama shi a kan hanyarsa ta zuwa Najeriya ta hanyar yada zango a kasar Masar.
Assir yana dauke da fasfo na jabu na kasar Falasdinu dauke da bizar Najeriya.
Wasu majiyoyi masu karfi sun shaida wa Aminiya cewa, fadar Shugaban kasa ta ji takaicin cewa mutumin da ke cikin jerin manyan ’yan ta’adda a duniya ya samu bizar shigowa Najeriya. Majiyoyin sun shaida wa wakilinmu cewa abin da ya fi bata wa gwamnati rai shi ne Al-Assir yana kokarin shigowa Najeriya ne a daidai da kassar nan ke yunkurin kawo karshen tu’annatin Boko Haram wadda ta jawo asarar dimbin rayuka da barnata dukiya.
Gwamnatin ta umarci Ma’aikatar Harkokin Waje da Hukumar Leken Asiri ta kasa (NIA) da Hukumar Shigi da Fici su hanzarta binciken lamarin tare da ba ta rahoto cikin gaggawa.
Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Bulus Lolo, ya ce gwamnati ta fara binciken kan bayar da biza ga dan ta’addan da ake nema don ziyartar Najeriya.
Lolo ya shaida wa manema labarai shekranjiya Laraba a Abuja cewa jami’an ofishin jakadancin Najeriya a Lebanon sun gana da mahukuntan kasar don duba lamarin. “Ni ma na fara nawa binciken. Na tattauna da karamin jakadanmu a Lebanon shi ma ya gana da da mahukuntan Lebanon. Jakadan ya ce yadda lamarin ke bayyana kafafen watsa labarai ba su bayar da hakikanin labarin ba. Ya bayyana wannan mutum dan Falasdinu ne da ke zaune a Lebanon na dogon lokaci. Yana da takardar zama dan kasa, kuma sananne ne Lebanon tana ba Falasdinawa ’yan gudun hijira takardun zama cikakkun ’yan kasarta.”
Ya ce “Wannan mutum yana daga cikin wadannan mutane, kuma ya kin yin amfani da sunansa na gaskiya ne abin da muke dubawa.”
Su ma Hukumar NIA da na shigi da fici sun fara nasu binciken kamar yadda Aminiya ta samu bayani.
Wani jami’in Hukumar NIA da ya yi magana da Aminiya kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce hukumar c eke da alhakin tsaron Najeriya daga waje kuma ta damu cewa dan ta’addan da ake nema ruwa a jallo yana shirin shigowa Najeriya.
Y ace tuni an fara binciken lamarin kuma ana daf da bankado yadda dan ta’addan da duniya k enema ya samu bizar zuwa Najeriya. Ya ce Najeriya tana da cikakken ofishin Jakadanci a Lebanon kuma a cewarsa akwai rukunin mutum uku da suke ba da biza a ofishin da suka hada da jami’an Ma’aikatan Harkokin Waje da na shigi da fici da na Hukumar NIA, kuma za a binciki yadda Al-Assir ya samu biza tare da hukunta duk mai hannu a ciki.
Yayin da Hukumar NIA ke bincikenta a nan cikin gida kuma Hukumar Tsaron kasa (SSS) za ta gudanar da nata binciken kamar yadda doka ta tanada.
Majiyoyinmu sun ce Shugaba Buhari ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan yadda aka bayar da biza ga dan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a tsawon shekaru.
Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakay sunanta ta ce Shugaban kasa ya damu da aukuwar lamarin, inda ta ce gwamnatin Buhari ba za ta zuwa ido a lokacin da hukumomin da ke kula da bayar da biza suke zagon kasa ga yunkurin gwamnati na kawar da ’yan ta’adda a kasar nan ba.