An fara gasar cin kofin kwallon kafa na dan Isan Saminaka

An fara gasar cin kofin kwallon kafa na dan Isan Saminaka kuma Mayanan Lere Barista Ibrahim Usman a babban filin wasan kwallon kafa na garin Saminaka da ke jihar Kaduna. Ita dai wannan gasar kwallon kafa, kungiyoyi 24 da suka fito daga sassan karamar hukumar Lere ne suke fafatawa. Da yake jawabi a lokacin da […]

An fara gasar cin kofin kwallon kafa na dan Isan Saminaka
An fara gasar cin kofin kwallon kafa na dan Isan Saminaka

An fara gasar cin kofin kwallon kafa na dan Isan Saminaka kuma Mayanan Lere Barista Ibrahim Usman a babban filin wasan kwallon kafa na garin Saminaka da ke jihar Kaduna. Ita dai wannan gasar kwallon kafa, kungiyoyi 24 da suka fito daga sassan karamar hukumar Lere ne suke fafatawa.

Da yake jawabi a lokacin da yake bude gasar, dan Isan Saminaka kuma Mayanan na Lere Barista Ibrahim Usman ya bayyana cewa ya sanya wannan kofi ne domin hada kan matasan karamar hukumar Lere. Don ganin an cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Har’ila yau ya ce sanya wannan kofi zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin yankin, domin masu saye da sayarwa za su rika zuwa wajen da ake buga wannan wasa, kuma mutane da dama za su halarci wajen daga kauyukan d ake yankin.
Ya ce a wannan kofi da ya sanya duk kungiyar da ta zo ta daya za ta samu kyautar kofi da Naira dubu 100. Haka kuma kungiyar da ta zo ta biyu za samu kyautar kofi da Naira dubu 50. kungiyar da ta zo ta uku kuma za ta samu kyautar kofi da Naira dubu 30. Sannan kuma duk kungiyoyi 24 da suka shiga wannan wasa za a baiwa dukkan ‘yan wasansu rigunan wasa.
Ya yi fatar wannan kofi zai zamanto sanadin dada kawo zaman lafiya da sada zumunci a tsakanin al’ummar wannan karamar hukuma.
Shi ma a nasa jawabin sabon dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakilyar mazabar Lere Alhaji Lawal Muhammad Rabi’u ya bada tabbacin cewa za su bada hadin kai da goyan baya wajen ganin an bunkasa harkokin wasannin motsa jiki a wannan yanki.
A ranar farko ta fara buga wannan gasa, kungiyoyin kwallon kafa na Rangers Hayin gada da Brige Piller Hayin gada ne suka fafata. An tashi wasan Brige Piller na da ci 3 yayin da Rangers ke da ci 1.