Yadda Musabakar Al-Kur’ani Karo Na 34 ke gudana A Yobe

Ranar Asabar za a karrama gwarazan wannan shekara na Gasar Al-Kur’ani ta Jihar Yobe.

Yadda Musabakar Al-Kur’ani Karo Na 34 ke gudana A Yobe

Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe ta bude Gasar Karatun Alkur’ani na Shekara karo na 34.

Mahadda Al’Kur’ani maza da mata 136 daga kananan hukumomi 17 na Jihar Yobe ne suke fafatawa a gasar, wadda ke gudana a garin Gashu’a, hedikwatar Karamar Hukumar Bade.

A ranar Asabar 19 ga watan Oktoba, 2024 idan Allah ya so, za a kammala gasar, tare da karrama gwarazan wanann shekarar.

Za a rufe taron ne a ranar Asabar bayan da aka shafe tsawon mako guda tana gudana a Kwalejin Ilimi ta Umar Suleiman da ke Gashua.

Da yake jawabi a wajen bude taron, babban sakataren hukumar, Malam Umar Abubakar, ya ce daukar nauyin gasar da gwamnatin jihar ke yi ya nuna jajircewar gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni na bunkasa ilimin zamani da Musulunci a jihar.

Babban sakataren wadda Kodinetan Makarantun Tsangaya da ke jihar,  Malam Usman Lawan, ya wakilta ya ce, gasar ba wai kawai za ta inganta neman ilimi ba ne, za kuma ta sanya kyawawan dabi’u a zukatan matasa da kuma inganta zamantakewa a tsakanin al’ummar jihar.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja