An fara ginin kasuwar albasa ta Aliero

karamar Hukumar Aliero mai Hedikwata a garin Aliero da ke Jihar Kebbi za ta kasha zunzurutun kudi sama da Naira miliyan 250 da domin gina sabuwar kasuwar albasa irin ta zamani a garin Aliero. Shugaban karamar Hukumar ta Aliero Alhaji Abubakar Sale Aliero ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake zagayawa […]

An fara ginin kasuwar albasa ta Aliero

karamar Hukumar Aliero mai Hedikwata a garin Aliero da ke Jihar Kebbi za ta kasha zunzurutun kudi sama da Naira miliyan 250 da domin gina sabuwar kasuwar albasa irin ta zamani a garin Aliero.

Shugaban karamar Hukumar ta Aliero Alhaji Abubakar Sale Aliero ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da yake zagayawa da yan’ jarida domin gane wa idonsu irin yadda aikin kasuwar ke gudana. Shugaban karamar hukumar ya ce ita wannan kasuwa sun ba da kwangilarta ne saboda kasuwar da ake ciki yanzu ta cunkushe sossai, idan aka ce maka lokacin cire albasa ya yi sai ka tausaya wa jama’a, saboda yawan cunkonson jama’a da abubuwan hawa, musamman manya motoci dake daukar albasa zuwa Kudanci kasar nan, kuma ga kasuwar a bakin babbar hanyar zuwa Sokoto. Alhaji Abubakar Sale Aliero ya ce, idan aka lura da jama’ar karamar hukumar yawancinsu duk manoman albasa ne, don haka ya zama wajibi a samar musu wadataccen fili da kuma shaguna domin ajiye amfanin gonarsu idan sun kawo kasuwa. Shugaban karamar hukumar ya ce samun ci gaba da ake yi da bunkasar tattalin arziki a karamar hukumar, shi ne ya zama wajibi, ta yadda dole a samu babban wuri da za a gina kasuwar irin ta zamani. A cewarsa, wanda aka bai wa wannan kwangila shi ne Abubakar Abba Aliero, shugaban kamfanin Labana, inda ya ce zai kammala aikin kasuwar a cikin watanni ukku zuwa hudu.