An fara gwajin rigakafin Ebola a Laberiya

A ranar Litinin ne aka fara gwajin rigakafin cutar Ebola mafi girma a kasar Laberiya. An dai shigar da allurar rigakafin cikin kasar ne cikin tsauraran matakan tsaro, sannan aka kai su boyayyun wurare a kasar da ke yankin Yammacin Afirka.Kamfanonin GSK da Merck ne suka samar da allurar riga-kafin. Masana kimiyya na Amurka da […]

An fara gwajin rigakafin Ebola a Laberiya
An fara gwajin rigakafin Ebola a Laberiya

A ranar Litinin ne aka fara gwajin rigakafin cutar Ebola mafi girma a kasar Laberiya.

An dai shigar da allurar rigakafin cikin kasar ne cikin tsauraran matakan tsaro, sannan aka kai su boyayyun wurare a kasar da ke yankin Yammacin Afirka.
Kamfanonin GSK da Merck ne suka samar da allurar riga-kafin. Masana kimiyya na Amurka da Liberia da ke cikin aikin yin riga-kafin sun ce za a yi wa ma’aikatan sa kan allurar ‘yar mitsitsiyar kwayar cutar Ebola a jikinsu, kuma wani likita dan kasar da shi ma yake cikin wadanda za a yi wa allurar ya ce babu hadari idan aka yi hakan saboda sinadarin da yake cikin rigakafin ba zai haifar da cutar Ebolar ba.
Ana sa ran kusan ma’aikatan lafiya guda dubu 30 da suka sadaukar da kan su ne za a yi wannan gwajin rigakafin a kansu. Fiye da mutum dubu 8 da 500 ne suka rasa rayukansu daga annobar Ebola wanda ta barke a wasu kasashen Guinea da Laberiya da kuma Saliyo a farkon bara. Kuma akwai akalla mutum dubu 22 da suka harbu da cutar. Har ila yau, a kasar Laberiya kawai fiye da mutum dubu uku da 500 ne suka mutu daga cutar. Amma alamu na nuna cewa kasar ta ciyu kan cutar bayan da ake ci gaba da samun raguwa daga masu fama da cutar a kasar a ’yan kwanakin nan.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce annobar ta shiga zango na biyu, inda a yanzu hankali zai fi karkata ne wajen kawar da ita baki daya.