An Fara Horas Da Likitocin Arewa Kan Dashen Ƙoda A Kano
Likitoci daga Arewacin Najeriya shida sun fara karɓar horo na musamman kan aikin dashen koda da yoyon fitsari a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH)
Likitoci daga Arewacin Najeriya shida sun fara karɓar horo na musamman daga kwararrun masu aikin dashen koda da yoyon fitsari a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Jihar Kano.
Horon da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) ke daukar nauyi, na da aniyar wadata likitocin da fasaha da gogewar da ta suka dace, tare da koyar da su amfani da sabbin kayan aikin zaman, don gudanar da dashen koda mai inganci.
Da yake jawabi a wajen bude taron, Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu, ya bayyana asibitin AKTH a matsayin zakaran gwajin dafi.
Ya bayyana cewa, an yi dashen koda sama da 100 tun lokacin da aka kafa cibiyar yin ta a asibitin a shekarar 2002.
Farfesa Sagir ya jaddada mahimmancin dorewa da kuma fadada wadannan ayyuka zuwa sauran cibiyoyin kiwon lafiya.
Mukaddashin Babban Daraktan Kula da Lafiya na AKTH, wanda Dokta Dalhatu Gwarzo ya wakilta, ya yaba bisa yadda taron ya gudana, tare da jinjinawa TETFUnd kan gudunmawar da take ke bayarwa ga ɓangaren dashen koda.
Umar Ali, wani dan kwangilar da ke samar da kayan aikin gwaje-gwaje a AKTH, ya bayyana cewa an kashe sama da Naira miliyan 200 wurin samar da kayan aikin dashen koda da na’urar nike tsakuwar koda.
Yanzu shekara 12 ke nan da fara aikin dashen koda a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin Dabo.