An fara kada kuri’a a zaben Ghana
A yau Laraba ne ake zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a kasar Ghana. Shekaru 25 ke nan da kasar Ghana ta koma turbar Dimukradiyya, kuma wannan shi ne karo na bakwai da al’umar kasar za su kada kuri’ar zaben shugaban kasa. A wannan zaben dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi […]
A yau Laraba ne ake zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a kasar Ghana.
Shekaru 25 ke nan da kasar Ghana ta koma turbar Dimukradiyya, kuma wannan shi ne karo na bakwai da al’umar kasar za su kada kuri’ar zaben shugaban kasa.
A wannan zaben dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin shugaba mai ci John Dramani Mahama na jam’iyyar NDC da Nana Akufo-Addo na jam’iyyar NPP, kamar yadda BBC ta bayyana
Akwai kuma wasu ‘yan takarar da za su wakilci jam’iyyu hudu, da kuma guda na indifand.
Ba dai wannan ne karo na farko da Nana Akufo-Addo mai shekara 72 ke tsayawa takarar shugabancin kasar, karo na uku kenan da yake neman kujerar.