An fara kokowar neman sarautar Olubadan a Ibadan
Kwanaki uku da mutuwar Olubadan, Oba Samuel Odulana, an samu ’yan takara biyu suna kokowar darewa kujerar sarautar Olubadan na Ibadan, duk kuwa da cewa a can baya, ba a cika samun rikici ko takara wajen nada sarautar Olubadan din ba, kasancewar ana duba mukamin sarauta ne a tsarin wanda za a nada, wato, akan […]

Kwanaki uku da mutuwar Olubadan, Oba Samuel Odulana, an samu ’yan takara biyu suna kokowar darewa kujerar sarautar Olubadan na Ibadan, duk kuwa da cewa a can baya, ba a cika samun rikici ko takara wajen nada sarautar Olubadan din ba, kasancewar ana duba mukamin sarauta ne a tsarin wanda za a nada, wato, akan nada wanda yake rike da mukami na kusa da Olubadan ne a yayin da mai rike da sarautar ya kau.
Kamar yadda al’ada ta tanatar, Balogun na Ibadan, Saliu Adetunji ake sa ran zai gaji Olubadan, kasancewarsa mafi girma cikin jerin masu rike da mukaman sarautun gargajiya kusa da Olubadan.
Sai dai kuma an jiwo Otun Seriki na Ibadan, Chif Adebayo Oyedeji yana fadin cewa shi ne ya fi cancanta a nada domin ya gaji Olubadan din, wanda haka ke nuna cewa za a samu takara ke nan a wannan karon. Tuni ma har ya shigar da kara gaban Babban Jojin Jihar Oyo, Mai Shari’a Mukhtar Abimbola, inda yake neman Gwamnatin Jihar da kwamitin nada sarautun gargajiya na masarautar da su nada shi a matsayin Olubadan da zai gaji kujerar Oba da ya rasu.
Kafin rasuwar shi Olubadan, shi ne ya daga martabar shi Saliu Adetunji zuwa sarautar Balogun na Ibadan, matakin da wasu ke ganin tamkar ya nada magajinsa ne, kafin mutuwarsa.
Aminiya ta kalato cewa, tun daga ranar Larabar da ta gabata ce ma aka fara murna a gidan shi Adetunji, dan shekara 87 saboda kyautata zaton cewa, shi ne zai gaji Olubadan din. Shi da kansa ma ya bayyana kansa a matsayin magajin Olubadan, wanda yake sa ran zai dare kujerar sarautar, bisa la’akari da tanadin al’adar nada sarautar.
Da yake jawabin ta’aziyyar rasuwar Olubadan Oba Samuel, Balogun na Ibadan, Saliu Adetunji ya ce: “Al’ada da tsarin sarauta ta tabbatar da cewa, kasancewata ni ne mutun na kusa a mukami ga Olubadan, ni ne zan kasance Olubadan da za a nada. Ina rokon Allah Ya jikan marigayi Olubadan. Shi ya kasance mutum mai ban mamaki, wanda ke nuna kauna ga kowa. Ina kira ga al’ummar Ibadan da ma baki da su sanya tsammanin mulkin adalci daga gare ni da yardar Allah.”
A yammacin ranar Talatar da ta gabata ne, Allah Ya yi wa Olubadan na Ibadan, Oba (Dakta) Samuel Odulana Odugade rasuwa a cikin gidansa da ke unguwar Monatan a Ibadan. Ya mutu yana da shekaru 101 wanda yasa aka soke yin bikin cika shekaru 102 da aka shirya yi a cikin watan Afrilu mai zuwa.
Marigayin shi ne Olubadan na 40 da ya hau sarauta a shekara ta 2007, a lokacin yana da shekaru 93. Ya yi aikin soja a shekara ta 1939 a lokacin Yakin Duniya na II. Ya rike mukamin karamin Ministan kwadago a shekara ta 1964 a lokacin da ya jagoranci tawagar wakilan Najeriya da suka halarci taron sake fasalin kundin tsarin mulki da aka yi a London. Yanzu haka an kai gawar marigayin zuwa Asibitin UCH da za a ci gaba da ajiye ta zuwa ranar da za a binne shi da fadar sarkin za ta ambata a nan gaba.
Marigayin ya fara shiga cikin jerin sunayen masu jiran gadon sarautar Olubadan ne a shekara ta 1972 a lokacin da ya zama Mogaji na zuriyar Ladunni da ke unguwar Igbo Elerin, wato mahaifarsa da ke cikin birnin Ibadan. Daga wancan lokaci ne ya rika samun karin girma har zuwa shekara ta 2007 da ya haye bias karaga. A zamanin mulkinsa ne aka fara gina fadar Olubadan ta dindindin da kowane sarki ya hau karaga zai rika zama da iyalansa tare da gudanar al’amuran mulki a cikinta, a maimakon zama da sarki yake yi a cikin gidan da ya mallaka a dalilin rashin fadar sarki ta dindindin.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan marigayin a ranar Larabar da ta gabata da safe, ya tarar da ’ya’yan marigayin da suka hada da Farfesa Femi Lana da Yarima Gbade Lana da Gimbiya Sade Bankole tare da manyan fadawa masu jiran gado da suka fara zaman makoki da karbar bakuncin mutane da suka fara kai gaisuwa gare su.
Babban limamin Ibadan, Sheikh Abdul-Ganiyu Abubakar Agbotomokekere, yana daga cikin manyan bakin da suka fara kai irin wannan gaisuwa.