An fara koyar da harshen Mandarin na China a makarantun Legas – Kwamishina
An fara koyar da harshen Mandarin na kasar China a wasu makarantu biyar da ke Jihar Legas, domin bunkasa koyon harsunan kasashen duniya, kamar yadda Kwamishinar ilimi ta jihar, Madam Olayinka Oladunjaiye ta bayyana wa taron manema labarai kan sauye-sauye da ci gaban da aka samu a ma’aikatarta.Kwamishinar ta ce makarantun sun hada da Bolade […]
An fara koyar da harshen Mandarin na kasar China a wasu makarantu biyar da ke Jihar Legas, domin bunkasa koyon harsunan kasashen duniya, kamar yadda Kwamishinar ilimi ta jihar, Madam Olayinka Oladunjaiye ta bayyana wa taron manema labarai kan sauye-sauye da ci gaban da aka samu a ma’aikatarta.
Kwamishinar ta ce makarantun sun hada da Bolade Junior Grammer School da Ikeja Junior Grammer Schiool da Immaculate High Comprehensibe da New Era Junior Girls School, da aka fara koyar da harshen kasar Sin, sai kuma makarantar Birch Freeman Senior High School, wadda aka fara koyar da harshen Jamusanci.
Madam Olayinka ta ce gwamnati ta fito da wannan tsarin ne domin ta kara yawan harsunan da ake koyarwa a makarantu, sannan duk dalibin da ya yi fice a daya dagas cikin harsunan sai gwamnati ta kara masa kwarin gwiwa domin ya karanta shi zuwa matakin karatu na gaba, wanda har idan ta kai ya tafi daya daga cikin kasashen da ake magana da harshen.
Ta ce za a kara yawan makarantun ne ganin yadda ake samun yawan daliban da suka suna sha’awar koyon harsunan. Game da karin kudin makaranta a jami’ar Jihar Legas, Kwamishinar ta ce ba kanshin gaskiya a cikinsa, domin wadanda suke korafin sun kasa biya, gwamnati ta taimaka musu da kudin makarantar.
Ta ce kuma gwamnatin jihar ta bukaci daliban da su je su yi shawara nawa suke ganin za su iya biya a matsayin kudin makaranta, idan har sun ce wanda gwamnati ta dan kara ya yi yawa, kuma har yanzu su ake jira, domin gabatar da wannan matsaya da suka cimmawa, ‘za ta duba da idon basira.’
Kwamishinar ta yaba nasarar da aka samu a makarantar koyon sana’a da gwamnatin ta bude, wadda da farko da kyar aka samu dalibai cikinta yau tana da dalibai 250, kuma sun yi rawar gani a jarrabawar farko da suka yi inda kashi 98 cikin 100 ne suka samu nasara.