An fara mayar wa alhazan bara ragowar kudinsu a Filato

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato ta fara mayar wa alhazan jihar na shekarar da ta gabata sauran kudinsu. Babban Sakataren Hukumar, Barista Auwal Abdullahi ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos. Ya ce game da mayar wa alhazan Jihar Filato na bara sauran kudadensu. A matsayinsa na […]

An fara mayar wa alhazan bara ragowar kudinsu a Filato
An fara mayar wa alhazan bara ragowar kudinsu a Filato

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato ta fara mayar wa alhazan jihar na shekarar da ta gabata sauran kudinsu.

Babban Sakataren Hukumar, Barista Auwal Abdullahi ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos.

Ya ce game da mayar wa alhazan Jihar Filato na bara sauran kudadensu. A matsayinsa na Sakataren Hukumar, ya amince a mayar wa dukan alhazan da suka biya Naira miliyan daya da rabi sauran kudinsu.

Ya ce hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda a bara an biya kudin kujera kan Naira miliyan daya da dubu dari hudu da saba’in da wani abu ne a jihar. Ya ce don haka za a mayar wa duk Alhajin da ya biya Naira miliyan daya da rabi rarar Naira dubu 28.

“Akwai alhazan bara sama da 90 da za a mayar musu cikon kudi. Kuma an fara biyan wadannan kudade tun a makon jiya,” inji shi.

Barista Auwal ya ce maniyyata aikin Hajji na  bana a Jihar Filato sun fara ajiyar kudaden kujerunsu.  Ya ce wadansu sun fara ajiye Naira miliyan daya, wadansu Naira dubu 500. Kuma zuwa yanzu an samu maniyyata da dama da suka fara ajiye kudinsu a jihar.

Ya yi kira ga maniyyata daga jihar su yi kokari su zo su biya kudinsu, domin tuni hukumar ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana. Ya ce sun tattauna da masu masauki da abinci a Kasa Mai tsarki. Ya ba da tabbacin cewa hukumar za ta tanadar wa Alhazan Filato gidaje masu kyau da masu dafa abinci, don ganin sun yi aikin Hajji cikin natsuwa da kwanciyar hankali.