An fara rububi a kan Paul Pogba
Manyan kulob a kasashen Turai ne da suka hada da Real Madrid da FC Barcelona na Sifen da Manchester City na Ingila da kuma Paris Saint Germain (PSG) na Faransa ne suka fara rububi a kan dan kwallon Jubentus na Italiya Paul Pogba. Paul Pogba, dan kimanin shekara 22, da alama babu dan kwallon da […]
Manyan kulob a kasashen Turai ne da suka hada da Real Madrid da FC Barcelona na Sifen da Manchester City na Ingila da kuma Paris Saint Germain (PSG) na Faransa ne suka fara rububi a kan dan kwallon Jubentus na Italiya Paul Pogba.
Paul Pogba, dan kimanin shekara 22, da alama babu dan kwallon da zai kama kafarsa a wajen tsada a kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo a bana, ganin yadda dan kwallon yake tashe.
dan kwallon, wanda ya taba buga wa kulob din Manchester United na Ingila, ya haskaka a kakar wasa ta bana, bayan ya taimaka wa kulob din Jubentus lashe manyan kofuna biyu da suka hada da kofin kalubale na Italiya da kuma gasar rukunin Italiya da aka fi sani da Serie A. Haka kuma dan kwallon ne ya taimaka wa kulob din kai wa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) a bana, inda kulob din FC Barcelona ya doke shi a wasan da ci 3-1.
Kulob din Real Madrid ya ce yana son ya dauke Pogba ne don ya karfafa ’yan wasan tsakiyarsa don ya tunkari kakar wasa mai zuwa. Kulob din ya fara shirin cefano zaratan ’yan kwallo ne kafin a fara kakar wasa mai zuwa tun bayan ya raba gari da tsohon kocinsa Carlo Ancelotti.
FC Barcelona kuma ta ce, idan ta samu Paul Pogba kakarta ta yanke saka. Kulob din ya ce idan Pogba ya hadu da zaratan ’yan kwallonsa irin su Lionel Messi da Neymar da Surez, ko shakka babu zai dade yana jan zarensa a fagen kwallo a ciki da kuma wajen Sifen. Kulob din Manchester City na Intgila kuma yana hasashen idan ya samu Pogba, to ba zai samu matsalar ’yan kwallon da ke buga masa kwallo a tsakiyar fili ba. Kulob din ya ce ganin yadda dan kwallonsa Yaya Toure ya yi sanyi kuma mai yiyuwa ma ya canza sheka kafin a fara kakar wasa ta bana, wannan ta sa ya yanke shawarar fara zawarcin Pogba, don kada a yi masa sakiyar da ba ruwa. Haka abin yake ga kulob din PSG na Faransa, inda kulob din yake kokarin ya cefano zaratan ’yan kwallo a ko’ina suke a duniya don ganin ya cigaba da haskakawa. Hasalima, hakan na daga cikin dalilan da ta sa ake damawa da PSG a fagen kwallo a wannan lokaci.
Sai dai ya zuwa yanzu kulob din Jubentus ya ce da wuya ya saki Pogba don yana bukatarsa. Amma dan kwallon ya nuna ba shi da sha’awar cigaba da zama a kulob din don haka yake tunanin ya canza sheka.
Sai dai rahotanni sun tabbatar kulob din Jubentus ba zai sayar da Paul Pogba a kasa da Fam miliyan 60 kwatankwacin Naira Biliyan 18 da miliyan 60 ga duk kulob din da yake bukatarsa ba.