An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano
Mahmud ya shaida wa wakilinmu cewa yadda ya yi watsi da tsohuwar sana’arsa ta sayar da lemon kwalba ya rungumi harkar hayar Fawa-bank
A yayin da matsalar rashin wutar lantarki da matsalar kwacen waya ke ci gaba da ci wa mutane tuwo a kwarya a sassa daban-daban na Jihar Kano, wasu matasa a Unguwar Bachirawa Kwanar Ungogo sun samu wata sabuwar hanyar kasuwanci da ke taimaka wa jama’a tare da samar musu da kudaden shiga.
Matasan su uku suna ba wa jama’a hayar macajin waya na tafi da gidanka da aka fi sani da suna Fawa-bank na tsawon awa 24, duk da cewa kudin Fawa-bank guda yana kaiwa kimanin Naira 10,000.
Wakilinmu ya ziyarci inda matasan suke gudanar da wannan sabuwar sana’a mai kama da almara, don jin yadda suke samun kudaden shiga ba tare da wani kalubale ba.
Biyu daga cikinsu, Mahmud Sulaiman Bawa da Abubakar Haruna Nasir, sun bayyana yadda suka fara sabuwar sana’ar, yadda suke gudanar da ita, da kuma karbuwarta a wurin jama’a.
Na watsar da tsohuwar sana’ata — Mahmud
Mahmud ya shaida wa wakilinmu cewa yadda ya yi watsi da tsohuwar sana’arsa ta sayar da lemon kwalba ya rungumi harkar hayar Fawa-bank a Jihar, Kano, wadda take yawan fama da matsalar rashin wutar lantarki da kuma fashin waya.
- ’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi
- An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka
“Ina harkar sayar da kayan lemon kwalba sai aka zo aka yi min tallar harkar Fawa-bank. Kamfanin Mopo suka zo suka same ni saboda sun ga wajena fuska ce mai kyau.
“Da farko suka ce, na san wannan abun? Na ce ban sani ba, sai suka ce suna so su dauke ni na zama wakilinsu. Sai na ce to amma a lokacin na ce masallaci zan je, idan na dawo zan same su.
“Ni a Kwanar Ungogo nake harkar sayar da kayan lemon kwalba suka zo har shagona. Sai na samu abokina na yi masa bayani, sai ya ce, zai yi harkar, sai muka je mu biyu suka yi mana horo kan yadda ake amfani da Fawa-bank din, yadda za mu saka caji, suka nuna mana komai a game da Fawa-bank din.”

Yadda muke bayar da hayar Fawa-bank
Ganin yadda suke bayar da hayar Fawa-bank wadda kudinsa ya kai kai kimanin Naira 10,000 na tsawon awa 24, Aminiya ta tambayi Mahmud game idan ta bace, da kuma yiwuwar wadanda suka karbi hayar su tafi da na’urar.
“Ni da kaina abin ya ba ni mamaki da farko, domin na yi mamakin ta yaya za a ce Fawa-bank sai da waya za a kunna shi?
“Ko me mutum zai yi ba zai kawo ba, ko wayoyi dari mutum zai sa ba zai kawo ba, sai mutum ya zo na kunna masa, har da fitila dole zai yi. Idan ban kunna wa mutum ba, ba zai taba yi ba, ko dauka mutum ya yi ba zai yi amfani ba,” in ji shi.
Mahmud ya ce, “kalubalen da mutane suke tunani shi ne idan aka karba za a gudu da shi. To idan an karba, dole sai mu za mu iya kunna maka shi. Mu za mu kunna maka da waya, akwai wata manhaja wadda da ita za a kunna wa mutum.
“Don haka abu na farko idan ka zo za mu yi maka rajista da shi, idan caji ya kare zai nuna maka launin ja a kai, dole mutum zai dawo da shi mu zo mu sauke mu bai wa mutum wani. Yana yin sa’o’i 24 a wurin mutum kuma zai caja waya sau hudu zuwa biyar,” in ji matashin.
Da yake karin bayani kan tsaron da ke tattare da na’urar, ya ce, “dole mu za mu kunna wa mutum, don bai isa ya saka caji ba ko a kunna fitila ba, kuma mutum bai isa ko wani waje ya kai caji ba.
“Sa’annan da lokacin da mutum ya karba ya zagayo zai nuna mana, zai sauka ya daina bayar da caji, zai nuna ga wani lokacin dawo da Fawa-bank dinsa ya yi, zan gani zan nemi mutum ko in kira shi a waya tun da ina da bayanansa ko lambar waya da adireshinsa da hotonsa.
“Zan kira mutum in ce wane lokacinka ya yi, zai ce, to zai dawo da shi. Muna bai wa mutane har wanda ba mu sani ba kawai idan ya bata ne mutum zai biya Naira 15,000.”
Ya ce, har yanzu mutane suna mamakin harkar, “wasu ba sa yadda cewar gaske ne, don har wasu ake aiko min su duba su gani ko gaske ne.”

Girman sana’ar hayar Fawa-bank a Kano
Matashin ya bayyana cewa, su uku da suke sana’ar a Kano, Kamfanin Mopo ya ba kowannensu Fawa-bank akalla guda 73.
Ya ci gaba da cewa, sabanin harkar cajin waya, wadda yawanci ana bukatar a tara da yawa kafin a kunna inji a fara caji, “A cikinmu ko guda daya aka dawo mana da shi za mu iya saka cajinsa.
“Kuma kowa a cikinmu yana da shaidarsa a jiki. Kowa nenmu Ungoggo ne a jikin nasa, amma nau’in da aka rubuta na kowa ya bambanta—wani ja, wani kore, wani ruwan dorawa.”
Ya ce, sukan bayar da haya a kan Naira 300, “wani wajen suna bayarwa a kan 400 har tsawon sa’o’i 24, mu da yake muna kiran kwastoma ne muna bayar da shi kan Naira 300.
Matashin dan kasuwan ya ce, kawo yanzu babu wani kalubale da ya taba samu a sabuwar sana’ar tasa, wadda ya ce, ta kawo wa jama’a sauki, musamman ganin yadda ake fama da matsalar kwacen waya a Kano.
“Har yanzu dai babu ko mutum daya da ya ba mu matsala, lokaci yana yi mutum zai dawo da shi. Mutum yana kawowa zan sauke, idan yana son wani sai in ba shi. An samar wa mutane sauki ne, an yi Fawa-bank din zai iya caja waya hudu har zuwa biyar.
“Mun samar wa mutane sauki, mutum a gida zai caja wayarsa, wasu masu manyan wayoyin ba su son fitowa da su musamman a wuraren da ake kwacen waya. To shi ya sa aka kawo wannan abun cikin sauki hankalin mutum a kwance, idan ma na matar mutum ne, zai saka caji hankalinsa a kwance.”
Game da korafin masu karbar haya, matashin ya ce, “kowa ya karba sai ya ce, ya ji dadi. Ba ma karbar korafi kowa idan ya karba yana jin dadinsa.”
Sai dai ya ce, a halin yanzu sun takaita sana’ar zuwa unguwarsu ne kawai. “Mutane suna ta aiko mana daga unguwa-unguwa, wani ma daga Dawanau wani daga Rijiyar Lemo, babu daga inda ba ma jin kira, kuma mu dole a tsarin da muke da shi, a iya yankinmu za mu bayar, sai dai idan mutum ya karba zai iya tafiya fa shi ko’ina yake so.”
Ya ce, sabon kasuwancin ya kawo sauki, idan mutum yana kasuwanci ba sai ya kai wayarsa wajen caji ba, ga shi kodayaushe za a iya neman sa, “yanzu waya ta zama kamar rayuwar mutum koyaushe tana tare da mutum ko barc ci mutum ya yi, ya laluba ya ji bai ji wayarsa ba zai mike.”

Tsarin ya takaita a unguwa guda
Game da tsarin da ake bayar da hayar, Mahmud ya ce ba su amince na’urar ta yi fiye da kwana guda a hannun mutum ba.
“Da yake muna da hoton duk wanda ya karba, to idan mutum ya kawo abun hannun da ake bayarwa da Power Bank din, idan muka duba ba hotonsa ba ne, ba ma ba shi.
“Saboda akwai wanda zai jefar da abun hannun da muke bayarwa wajen alwala ko wani abu. Sai mun yi waya da ainahin wanda ya karba ya ce shi ya turo mutum sai mu dora mu karbi kudinmu mu ba shi Power Bank.”
Wakilinmu ya tambaye yi yadda suke yi da kudin da kuke karba, inda matashin ya shaida masa cewa, “ba mu muke rikewa ba, akwai asusu na wallet da yake cikin wayarmu. Muna bayar da shi (na’urar) a kan farashin Naira 300, suna cire nasu, su bar mana namu a cikin wallet din.
“Mu kuma muna tara shi, idan ya kai wani lokaci akwai asusu da suka bude mana sai a saka mana a ciki mu cire kayanmu.”
Yadda ake rajista
Ya a yayin yi wa mai son karbar haya rajista, bayansa da ake karba sun hada da cikakken suna, kwanan watan haihuwa, sana’a da kuma adireshi sai lambar waya, “Ko da mutum ya yi latti ko ya manta, mu za mu kira shi saboda mu lokaci yana yi za mu gani a nan.
“Saboda haka ana daukar wasu kudi a wajenmu idan lokaci ya yi mutum bai dawo da shi ba, suna daukar Naira 50 ko 100 a cikin wallet dinmu.”
Sia dai ya ce su ba su kara kudin latti ba a yanzu, “saboda kiran kwastoma muke yi, so muke mu kai wani matsayi da zai sa a ce kamfanoni sai sun jingina a jikinmu nan gaba.”
Na ji dadinsa — Isma’il
Wakilimu ya hadu da wani wani wanda ya zo karbar hayar Fawa Bank a shagon, Isma’i Abdulkadir, wanda ya bayyana cewa ya kai kwana hudu a jere yana zuwa karba, kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu.
“Tun da na amsa, wasu na gani muna zuwa mu amsa suna jin dadinsa, kullum za su mu zo mu karba mu dawo da shi kuma mu sake amsar wani, saboda muna jin dadinsa sosai.” a cewa Ismai’l, wanda ya ce takan cika masa wasa fiye da sau hudu.
Ya kara da cewa, “Yana da inganci, gaskiya ni ba ya ba ni wata matsala. Yana min abubuwan da nake so, zan cika wayata, idan na shanye in kara cikawa, har ya cika min waya sosai ma.”