An fara sayar da alkalamin itaciyar tsunami kan Naira miliyan 9 a Japan

Kamfanin kera kiayan kawa na alfarma, zai fara sayar da alkalamin da kirar darajarsa ta kai Dala dubu hudu da 400, kuma an samar da shi ne daga itacen bishiyar da ta tsira daga hadarin ambaliyar tsunami da aka yi a shekarar 2011; kuma za a sarayar da kashe 20 cikin 100 na abin da […]

An fara sayar da alkalamin itaciyar tsunami kan Naira miliyan 9 a Japan
An fara sayar da alkalamin itaciyar tsunami kan Naira miliyan 9 a Japan

Kamfanin kera kiayan kawa na alfarma, zai fara sayar da alkalamin da kirar darajarsa ta kai Dala dubu hudu da 400, kuma an samar da shi ne daga itacen bishiyar da ta tsira daga hadarin ambaliyar tsunami da aka yi a shekarar 2011; kuma za a sarayar da kashe 20 cikin 100 na abin da aka samu ga talakawa, kamar yadda wani jami’in kamfanin ya bayar da sanarwa.

Wannan labari ya fito ne a daidai lokacin da kasar Japan ke shirin yin bikin cikar shekara hudu da aukuwar ambaliyar tsunami, wadda ta ci rayuka sama da dubu 19, ta kuma mayar da dubban mutane suka rasa gidajensu. Wannan musifa ta ambaliyar tsunami ta haifar da asarar dukiya, wadda ba za a iya kimanta ta ba.
Daga cikin asarar da tsunami ta haifar, akwai fashewar tashar makamashin nukiliya, wadda tursasa mutane da dama suka gidajensu, wadanda har yanzu a tsugunne suka, a wuraren tsugunnar da wadanda suka rasa muhallinsu.
Wannan kamfani da ke kera alkalami da agogo na kasar Switzerland, ya yi amfani da katako da aka sarrafa daga itaciyar da ta rage a dajin Rikuzentakata da ke yankin Arewa maso Gabashin Japan, inda bishiyoyi sama da dubu 70 suka fadi, suka bi ruwa.
Wannan bishiya da aka yi wa lakabi da “’yar baiwa”, an sameta ta kusa mutuwa, har sai da aka kashe mata Dala miliyan da rabi, inda a halin yanzu ta zama wurin ziyara.
Lokacin hukumar birnin ta sare wannan bishiya, sai magajin garin Futoshi Toba ya roki reshen Kamfanin Switzerland da ke kera kayan kawa na alfarma, wadanda suka hada da alkamin rubu da agogo, da ya yi amfani da katakon itacen bishiya wajen kera alkalami, don tuna wa mutane wannan musifar da ta jikkata rayuwar al’umma, a cewar jami’in birnin.
Kamfanin Monthblanc ya kera akalla alkaluman rubu 113, inda yawan alkaluman ke nuni da jaddawalin 11 ga Maris daidai da ranar da musifar ambaliyar tsunami ta auku, kuma za a rika sayar da ita a kan farashin dubu 520 na kudin Yen, wanda ya yi daidai da Dalar Amurka dubu hudu wato daidai da Naira miliyan tara da dubu 680.
“Wannan bishiya ita kadai ta rage da take ba mu kwarin gwiwar tsallake hadarin wannan musifa,” a cewar Toba, lokacin da ya kira wani taron ’yan jarida.
“Kamfanin Montbalanc zai taimaka, kuma ina da tabbacin cewa duniya za ta dubi wannan musifa,” inji mai magasna da yawun kamfani a kasar Japan, inda ya bayyana cewa, tallafin kashi 20 cikin 100 da kamfanin ya bayar gudunmuwa ce don tallafawa ga aukuwar musifar.
Ya ce tsabagen tsadar kowane alkalmi da ake sayarwa kan Dala dubu hudu ya auku ne, saboda karancin kayan sarrafa hajar, “domin ba a yi su domin yin alkaluma ba.” Sai dai mai magana da yawun kamfanin ya ki bayyana kudin da aka kashe wajen yin kowane alkalami, ko kuma ribar nawa kamfanin zai ci a kowane ciniki.