An fara shari’ar Alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen

A yau Litinin an fara shari’ar Alkalin alkalan Najeriya mai shari’a Walter Onnoghen a kotun da’ar ma’aikata da ke Abuja. Duk da yake babban alkalin bai gurfana da kansa ba lokacin da ake ci gaba da shari’ar ta yau. Rahotanni na bayyana cewa, laifuka shida ake tuhumar Walter Onnoghen, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana […]

An fara shari’ar Alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen

A yau Litinin an fara shari’ar Alkalin alkalan Najeriya mai shari’a Walter Onnoghen a kotun da’ar ma’aikata da ke Abuja.

Duk da yake babban alkalin bai gurfana da kansa ba lokacin da ake ci gaba da shari’ar ta yau.

Rahotanni na bayyana cewa, laifuka shida ake tuhumar Walter Onnoghen, dukkaninsu da suka shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka, wanda hakan ya saba wa dokar tabbatar da da’a ta Code of Conduct Bureau kamar yadda gwamnatin tarayya ta zarginsa da aikata wa.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta