An fara shari’ar dan jaridar RFI a Kamaru
A karon farko an gurfanar da wakilin sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa (RFI) Ahmed Abba a gaban kotun soji tun lokacin da ya shiga hannun jami’an tsaro a birnin Maroua da ke kasar Kamaru a watan Yulin bara.Gabanin gurfanar da shi a ranar Talata, yana tsare ne a hannun jami’an tsaro ba tare da […]
A karon farko an gurfanar da wakilin sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa (RFI) Ahmed Abba a gaban kotun soji tun lokacin da ya shiga hannun jami’an tsaro a birnin Maroua da ke kasar Kamaru a watan Yulin bara.
Gabanin gurfanar da shi a ranar Talata, yana tsare ne a hannun jami’an tsaro ba tare da yin tozali da iyalinsa ba, ballantana lauyansa.
A baya Ministan Sadarwa kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya ce Jami’an tsaro na tatsar bayani daga gareshi, sai bayan sun kammala ne za su gurfanar da shi gaban kuliya.
Jami’an tsaron suna zargin Ahmed ne da hada baki da wasu ‘yan ta’adda biyu ‘yan asalin Najeriya wurin kai hari a Kamaru, sa’annan kuma da gaza sanar wa hukuma aikin ta’addancin. Kodayake, wanda ake zargin ya musanta duka tuhumar da ake masa.
Akan wadannan dalilan ne suka mika shi ga kotun soji wadda ita kuma bayan ta bude kundin wakilin na RFI, lauya mai kare Gwamnati shi ma sake jaddada aikata wadannan laifuffukan ya yi, inda ya kara da cewa Ahmed ya ki sanar da gwamnati shirin kai mata hari, a wani sashen kasa alhalin yana da masaniya a kai.
Hari la yau, su ma lauyoyin wanda ake tuhuma sun yi watsi da wadannan tuhume-tuhume. Daga bisani kuma sun yi korafi kan yadda ba a bi doka ba wajen tafiyar da shari’ar. A kan hakan ne suka nemi kotun ta soke sauraron karar.
Daga cikin ababan da lauyoyin Ahmed suka bayyana akwai garkameshi da aka yi a sirrance ba tare da iyali ko kuma lauyoyinshi sun kai masa ziyara ba. Sa’annan kuma babu wata takardar shaidar da ta nuna kara wa’adin tsare shi da aka yi bayan kwanaki 15 na farko. Har ila yau, akwai zargin azabtarwa da gwale-gwale da Ahmed ya sha a lokacin da yake hannun jami’an tsaro masu tatsar bayanai.
Lauyansa Me Charles Tchougang ya kara da cewa a lokacin da ya kai masa ziyara bayan an kai shi gidan wakafi, ya sameshi a daura da sarka.
An dai dage shari’ar zuwa ranar 28 ga wannan watan.
A ranar 14 ga watan Agustan bara ne aka mika shi ga barikin jami’an tsaro na Jandarma birnin Maroua, inda aka ajiye shi a cikin sirri har na tsawon watanni uku.
Hari la yau, kuma a ranar 13 ga watan Nobambar aka fiddashi daga birnin Maroua zuwa kurkukun da ake tsare wadanda ake tuhuma da aikata manyan laifuffuka da ke cikin Babban barikin Jami’an tsaro na birnin Yaounde.
A can ne dan jaridar ya yi zaman kwanaki 26, sai kuma a ranar 9 ga watan Disambar barar aka sake masa wuri zuwa gidan fursunan Yaounde, inda aka ware wani sashe guda na musamman domin ajiye wadanda ake zargi da laifukan da suka shafi kungiyar Boko Haram da ta’addanci.