An fara shari’ar Yunusa Dahiru a Bayelsa
A yau Talata ne aka fara shari’ar saurayin nan wanda ake zargi da guduwa da wata budurwa, ‘yar asalin Jihar Bayelsa, a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke garin Yenagoa na Jihar Bayelsa. Ana tuhumar saurayin Yunusa Dahiru ne da laifuka biyar wadanda suka hada da garkuwa da yarinya Ese Oruru da aikata zina […]


A yau Talata ne aka fara shari’ar saurayin nan wanda ake zargi da guduwa da wata budurwa, ‘yar asalin Jihar Bayelsa, a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke garin Yenagoa na Jihar Bayelsa.
Ana tuhumar saurayin Yunusa Dahiru ne da laifuka biyar wadanda suka hada da garkuwa da yarinya Ese Oruru da aikata zina da sauransu. Sai dai ya musanta duka zargin da ake masa.
A karshe kotun ta ki ba da belinsa kuma ta dage zamanta zuwa ranar Litinin mai zuwa.