…An fara tantance maniyyatan Jihar Kaduna

Ranar Larabar makon jiya ne Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ta fara tantance maniyyatan jihar sama da dubu biyar da ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin bana.Da yake kaddamar da fara aikin tantancewar a fadarsa da ke Kafancan, Mai martaba Sarkin Jema’a Alhaji Muhammadu Isah Muhammadu ya yaba wa hukumar kan fara shirin […]

…An fara tantance maniyyatan Jihar Kaduna
…An fara tantance maniyyatan Jihar Kaduna

Ranar Larabar makon jiya ne Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ta fara tantance maniyyatan jihar sama da dubu biyar da ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin bana.
Da yake kaddamar da fara aikin tantancewar a fadarsa da ke Kafancan, Mai martaba Sarkin Jema’a Alhaji Muhammadu Isah Muhammadu ya yaba wa hukumar kan fara shirin aikin Hajjin bana cikin lokaci, kuma ya roki maniyyatan jihar su kasance masu bin dokokin kasar Saudiyya sau da kafa.
Sarkin ya yaba wa gwamnatin jihar bisa taimako da kulawa da take ba Hukumar Alhazan Jihar inda ya ce haka na taimakawa wajen nasarar da hukumar ke samu a duk shekara.
A jawabin Shugaban Hukumar Alhazan Jihar, Alhaji Kabir kasim ya ce manufar tantance maniyyatan da hukumar ta fara ita ce domin a fahimci ko maniyyata sun fahimci bitar da aka kwashe watanni ana musu, amma ba domin a hana wani ko a hukunta shi ba.
Saboda haka ya roki maniyatan su ci gaba da bada goyon baya ga hukamar domin ta ci gaba da samun nasara.
Shi kuwa Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Addinin Musulunci, Alhaji Abdulrahman Mahmoud yaba wa gwamnati da kuma fadar ya yi kan goyon baya da suke ba hukumar.