An fara yunkurin cire Mu’azu daga shugabancin PDP

An fara wani sabon yunkuri na cire Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu daga matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa. A ranar Talata ce Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta fara sauraren wata kara da take neman a bayyana nada Mu’azu a matsayin shugaban jam’iyyar da zama haramtacce.Wani lauya kuma dan Jam’iyyar PDP mai suna Ezionye […]

An fara yunkurin cire Mu’azu daga shugabancin PDP
An fara yunkurin cire Mu’azu daga shugabancin PDP

An fara wani sabon yunkuri na cire Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu daga matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa.

A ranar Talata ce Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta fara sauraren wata kara da take neman a bayyana nada Mu’azu a matsayin shugaban jam’iyyar da zama haramtacce.
Wani lauya kuma dan Jam’iyyar PDP mai suna Ezionye Ndubuisi, wata biyu daga suka gabata ya bukaci Babbar Kotun Tarayya ta cire Mu’azu daga shugabancin jam’iyyar.
A wataa sabuwar kara da Emmanuel Onu, wanda shi ma dan Jam’iyyar PDP ne, yana rokon kotun ce da ta bayyana cewa takardar murabus din Bamanga Tukur da Shugaba Jonathan ya gabatar ga Kwamitin Zartarwar uwar jam’iyyar ya saba wa sassa na 47(5) da (6) tsarin mulkin Jam’iyyar PDP na shekarar 2012.
Onu kuma yana bukatar kotun ta bayyana nada Mu’azu a matsayin shugaban jam’iyyar a matsayin haramtacce da ya saba wa ka’idojin da sassa na 45(1) da (2) na tsarin mulkin Jam’iyyar PDP na shekarar 2012.
Wadanda ake kara sun hada da Jam’iyyar PDP da Ahmadu Mu’azu da kuma Hukumar Zabe ta kasa (INEC).
An nada Mu’azu a matsayin shugaban jam’iyyar ne a lokacin taron kwamitin zartarwar jam’iyyar na kasa a ranar 15 ga Janairu.
Mai karar ya kuma roki kotun ta soke nada Mu’azu a matsayin shugaban jam’iyyar saboda rashin bin tanadin sashi na 85 (1) na dokar zabe ta Najeriya ta 2010 da kuma sashi na 223 (1) na tsarin mulkin 1999, kuma yana bukatar kotun ta hanzarta dawo da Bamanga Tukur a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, ko kuma a Mataimakin shugaban ya jagoranci harkokin Jam’iyyar PDP har zuwa lokacin da za a bi ka’ida wajen zaben shugaban jam’iyyar na kasa kamar yadda doka ta tanada.
Onu ya kuma bukaci kotun ta dakatar da Mu’azu daga bayyana kansa a matsayin shugaban Jam’iyyar PDP, kuma ta hana Hukumar INEC hulda da shi a matsayin shugaban.