An fara zagayen karshe na sayar da tikitin kallon cin kofin duniya a Qatar
A baya dai, FIFA ta ce sama da tikiti miliyan 2.4 aka sayar
A ranar Talata ce aka fara sayar da tikitin zagaye na karshe na gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 da za a gudanar a kasar Qatar.
Kasashe 32 ne za su halarci gasar da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba mai zuwa, kuma za a taka wasan karshe ne ranar 18 ga watan Disamba.
- APC ta dage fara yakin neman zaben Shugaban Kasa har sai abin da hali ya yi
- Fiye da kaso 70 na Katsinawa na fama da matsanancin talauci – MDD
An dai fara sayar da tikitin ne tun karfe 09:00 na safe a agogon GMT, za kuma a kammala da zarar ya kare baki daya.
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) dai a baya ta ce a zagaye uku na sayar da tikiti, an sayar da sama da guda miliyan 2.4 na gasar a bana.
Haka kuma ta ce an sayar da tikiti 520,532 a tsakanin biyar ga watan Yuli zuwa 16 ga Agustan 2022.
Kimanin mutane 3,010,679 ne za su halarci kasar ta Qatar don kallon wasannin, inji FIFA.
FIFA ta kuma ce tikitin wasannin da aka fi saye sun hada da na karawar da Brazil da Kamaru da Serbia, da na Portugal da Uruguay, da Costa Rica da Jamus, da kuma wasan Australia da Denmark.
Ana sa ran gasar cin kofin duniya za ta jawo hankalin magoya bayanta fiye da miliyan 1.2 zuwa Qatar.
Masu shirya gasar dai sun ce za a samar da isassun masaukai ga dukkan magoya baya a kasar da tuni take dauke da mutum miliyan 2.8, duk da fargabar da mutane ke yi kan ba ta da isassun dakunan da za ta dauki jama’a.