An fara zanga-zangar goyon bayan Tinubu a Kano
Masu zanga-zangar goyon bayan Tinubu sun yi taro a Fadar Sarkin Kano da ke Nasarawa
Masu zanga-zangar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun fito kan tituna a Jihar Kano.
Masu wannan zanga-zanga suna yin ta ne a daidai lokacin da Najeriya ta dauki zafi da zanga-zangar nuna adawa da halin yunwa da tsadar rayuwa a kasar.
Masu wannan zanga-zanga sun fito ne ta titin Audu Bako da kuma Farm Centre suna bayyana adawa ga abin da suka kira zanga-zangar tashin hankali.
Sun kuma yi taro a Fadar Sarkin Kano da ke Nasarawa, inda suka saurari jawabai kan hanyoyin da za a magance matsalolin da ke addabar kasar.
- Jami’an tsaro sun yi harbi a Gidan Gwamnatin Kano
- Jerin zanga-zanga da suka girgiza Najeriya
- Zanga-zanga: Matasa da Jami’an tsaro sun yi sa-in-sa a Neja
Da yake musu jawabi, Abdullahi Muhammad Saleh ya ce , “Mun fito domin yaba ayyukan cigaban da Shugaba Bola Tunubu ya aiwatar.
“Muna jinjina masa da ya kafa Hukumar Kula da Cigaban Arewa Maso Yamma, wadda za ta kawo kyakkyawan sauyi a yankin.
“Babbar hanyar bayyana rashin jin dadi ita ce tattaunawa, ba fito-na-fito da gwamnati ba.
“Kowa na cikin wannan mummunan yanayi amma zanga-zanga ba ita ba ce mafita.
“Mu fara neman a zauna lafiya sannan mu hada kai wajen tattaunawa da gwamnati ba, don shawo kan matsalolin namu
“Ba ma son marasa kishin kasa da bata-gari su kwace wannan zanga-zanga.
“Mu dai muna goyon bayan wannan gwamnati saboda mun san abubuwan da take yi.”