An farfado da bikin al’adu na kamun kifi a Bade bayan shekara 25

Bikin al’adun kamun kifi na al’ummar Bade a Jihar Yobe, biki ne mai tsohon tarihi da aka faro sama da shekara 50 da suka gabata, amma ya gamu da cikas aka dakatar shekara 25, sai bana aka farfado da shi don inganta al’adun al’ummar Badawa. Bikin karo na 38 da aka gudanar gami da wasannin […]

An farfado da bikin al’adu na kamun kifi a Bade bayan shekara 25

Bikin al’adun kamun kifi na al’ummar Bade a Jihar Yobe, biki ne mai tsohon tarihi da aka faro sama da shekara 50 da suka gabata, amma ya gamu da cikas aka dakatar shekara 25, sai bana aka farfado da shi don inganta al’adun al’ummar Badawa.

Bikin karo na 38 da aka gudanar gami da wasannin gargajiya a ranakun Asabar da Lahadin makon jiya da suka gabata ya kayatar sosai.

A ranar Asabar an gudanar da raye-raye da wasanni iri-iri a kofar Fadar Mai Bade Alhaji Abubakar Umar Suleiman, bikin ya yi armashi inda aka motsa wa Badawa al’adunsu da aka jima ba a yi ba.

Makada da masu rawa sun cashe inda aka bayyana tarihin rike al’ada a matsayin abin koyi da cewa duk wanda ya tashi bai da al’ada bai san tushensa ba.

A ranar Lahadi kuma, Badawa da ’yan kallo daga ciki da wajen Jihar Yobe sun dunguma zuwa Kogin Alkamaran a garin Gogaram a Karamar Hukumar Jakusko don ganin gasa iri-iri a ruwa har da gasar kamun kifi.

Da yake jawabin maraba da baki, Mai Bade Alhaji Abubakar Umar Suleiman gode wa al’umma ya yi a madadin Masarautar Bade, kan halartar bikin karo na 38 da aka jima ba a yi ba.

Mai Bade ya ce a baya duk shekara ake bikin tun zamanin kakansa na Sarki lokacin Jihar Yobe na Jihar Borno,  har mahaifinsa ya zama Sarki ba a fasa ba sai daga baya aka samu matsala, amma yanzu da hadin kan Gwamna Mai Mala za a ci gaba da gudanar da shi duk shekara.

Mai martaba Mai Bade Alhaji Abubakar Umar ya kara da cewa gudanar da biki irin wannan zai taimaka wajen kara hada kan al’ummar kasar Bade da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sai ya yi roko ga Gwamnan Jihar ya taimaka wajen samar da hanyar mota daga garin Amshi zuwa Gogaram don sauwake wa mutane shiga garin har zuwa bakin kogi Kanda da akalla ta kai kilomita 100.

Ya ce sun taba magana da Ministan Ruwa don yashe kogin don a samu ya fadada shi ana kama manyan kifi.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Mai Mala Buni cewa ya yi ganin an dade ba a yi wannan biki ba haka zai kara hada kan jama’ar Bade da Jakusko da kara sanin muhimmancin al’adun gargajiya.

Gwamna Buni ya ce bisa albarkacin wannan kogi Jihar Yobe za ta kara samun kudin shiga.

Ya bai wa Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci ta Jihar umarnin ta yi dukkan mai yiwuwa don jihar ta kara samun kudin shiga daga Kogin Alkamaran.

Sannan ya ce tunda bikin na gasa ne, yana yi wa wadanda suka shiga fata alheri.

Shugaban Majalisar Dattawa Dokta Ahmed Ibrahim Lawan cewa ya yi wannan biki na bana ya yi armashi ganin an dade ba a yi ba kuma shi ma zai kara taimakawa don ganin ana yin bikin duk shekara.

Sanata Ahmed Lawan ya ce zai yi iya kokarinsa don ganin an ci gaba da bunkasa al’adun gargajiya, kuma batun hanya daga garin Amshi zuwa Gogaram da Mai Bade ya yi magana za a yi domin yanzu haka an samar da wutar lantarki a yankin.

A lokacin bikin an gudanar da wasanni iri-iri na yara ’yan shekara bakwai a cikin ruwan na wasan ninkaya da goyon biyu da goyon daya a kan gora a haye ruwa na maza da mata, sannan aka kare da gasar kamun kifi a tsakanin Sarkin Ruwan Gashuwa da Sarkin Ruwan Gogaram inda Sarkin Ruwan Gashuwa Mohammad Ibrahim Mohammad ya lashe gasar da babban kifi mai nauyin kilo shida.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya mika masa kyautar Keke NAPEP, shi kuwa Sarkin Ruwan Gogaram aka ba shi Naira dubu 300.