An farke cikin mai juna biyu an sace dan tayin

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mai ma juna biyu, suka farke cikinta, suka dauke dan tayin

An farke cikin mai juna biyu an sace dan tayin

Wata mace mai juna biyu (Tsohuwar ajiya)

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kashe wata mai ma juna biyu, suka farke cikinta sannan suka dauke dan tayin da ke ciki.

Rahotanni sun ce an tsinci gawar matar mai juna biyu ne a yashe a kan wani juji a Rukunin Gidajen Alkalai da ke Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai.

Aminiya ta gano cewa tsinci gawar mai juna biyun ce kwana kadan bayan ’yan sanda sun tsinci gawar wata dalibar jami’a a unguwar.

Wani ganau da ya ce a boye sunansa ya bayyana cewa mai juna biyun da aka tsinci gawarta an farke cikinta an tafi da dan tayinta, wata mai tabin hankali ce da ke yawo a yankin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an dauke gawar zuwa mutuwari.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan