An fatattaki mawakiya Rihanna daga masallaci a Dubai

A farkon makon nan ne hukumomi a birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddar Daular Larabawa suka umarci mawakiya Rihanna da ta fita daga harabar wani katafaren masallaci.Mawakiyar, ta kai ziyara ne kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda cikin yawace-yawacenta ta shiga harabar masallacin Shaikh Zayyad ranar Asabar da ta gabata, inda ta rika daukar hotuna […]

An fatattaki mawakiya Rihanna daga masallaci a Dubai

A farkon makon nan ne hukumomi a birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddar Daular Larabawa suka umarci mawakiya Rihanna da ta fita daga harabar wani katafaren masallaci.
Mawakiyar, ta kai ziyara ne kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda cikin yawace-yawacenta ta shiga harabar masallacin Shaikh Zayyad ranar Asabar da ta gabata, inda ta rika daukar hotuna daban-daban. Hakan ya kai ta har ta shiga wani wuri na musamman a masallacin, inda ba a barin masu kai ziyara zuwa. Hakan ya sanya hukumomin masallacin suka ankara da halin da mawakiyar take ciki.
Hukumomin masallacin sun fitar da sanarwa a Lahadin da ta gabata, inda kamar yadda jaridar ‘Gulf News’ ta ruwaito, sun bayyana cewa duk da cewa ba a hana masu ziyara su ziyarci masallacin ba, koda kuwa wane addini suke bi, amma irin yadda Rihana ta rika daukar hotuna daban-daban a wurare daban-daban na masalacin, hakan ya zama tamkar cin zarafi ne ga wurin ibadar.
Mawakiyar dai ta dauki hotunan ne cikin dogayen riguna bakake, sannan kuma ta watsa su cikin shafinta na intanet na Instagram.