An fatattaki mayakan IS a Masar

A jiya Alhamis ne jami’an tsaro a kasar Masar suna ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar IS masu da’awar kafa kasar Musulunci wadanda suka far ma yankin arewacin Sinai na kasar. Rundunar sojin kasar ta ce ba zata daina bude wuta a kan wadanda ta kira ‘yan ta’adda ba har sai ta kawar da su […]

An fatattaki mayakan IS a Masar
An fatattaki mayakan IS a Masar

A jiya Alhamis ne jami’an tsaro a kasar Masar suna ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar IS masu da’awar kafa kasar Musulunci wadanda suka far ma yankin arewacin Sinai na kasar.

Rundunar sojin kasar ta ce ba zata daina bude wuta a kan wadanda ta kira ‘yan ta’adda ba har sai ta kawar da su daga yankin, kamar yadda BBC ta ruwaito.
A shekaranjiya Laraba ne dai mayakan IS suka kaddamar da manyan hare-hare kan jami’an tsaro a yankin.
Jiragen saman yakin Masar sun ci gaba da lugudan wuta a daren shekaranjiya Laraba, kwana daya bayan wani kazamin fada daya barke, ya yi sanadiyar mutuwar mayakan da dama.
Wannan dai shi ne harin da suka kai da yafi daukan lokaci kuma a wurare da yawa, da suka hada da wuraren duba ababen hawa, da ofishin ‘yan sanda da kuma garin Sheikh Zuwaid.
Kakakin sojin kasar Brigediya Mohammed Samir ya ce sun kashe akalla mayakan kungiyar guda 100.
Wani labarin kuma, a jiya Alhamis Ministan Tsaron Birtaniya Michael Fallon zai ba da shawara a gaban majalisar dokokin kasar kan sake duba matakin da kasar ta dauka na kin amincewa da kaiwa mayakan IS reshen kasar Siriya hari.
Mista Fallon ya ce akwai yiwuwar cewa harin da mayakan IS din suka kaiwa wasu masu ’yan yawon bude ido ‘yan Birtaniya a kasar Tunisiya ranar Juma’a da ta gabata, an shirya shi ne a birnin Rakka na kasar Siriya.