An fi kamuwa da cutar Ebola daga 1 gawa – Hukumar WHO
Shugaban kasa Jonathan Goodluck ya bayyana cewa daga bayanan da ya samu, kashi 60 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar Ebola, sun samu cutar ne ta hanyar hulda da gawa a yayin da suke kokarin yin jana’izarta, saboda haka ya bukaci ’yan Najeriya su rika lura a yayin gudanar da jana’izar ’yan uwansu.Ya […]


Shugaban kasa Jonathan Goodluck ya bayyana cewa daga bayanan da ya samu, kashi 60 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar Ebola, sun samu cutar ne ta hanyar hulda da gawa a yayin da suke kokarin yin jana’izarta, saboda haka ya bukaci ’yan Najeriya su rika lura a yayin gudanar da jana’izar ’yan uwansu.
Ya ci gaba da cewa, bayanai sun nuna cewa marigayi Patrick Sawyer da ya shigo Najeriya da cutar Ebola daga kasar Liberiya ya kamu da cutar ce a lokacin da yake binne ’yar uwansa da ta rasu ta hanyar cutar. Kuma maimakon ya bari a bincike shi, sai kawai ya taho Najeriya ya yada cutar ga wadansu.
Dangane da haka ne Shugaba Jonathan ya ce zai fi dacewa mutane su rika binne gawa a wurin da mamacin ya rasu maimakon daukarta daga wani bangare zuwa wani bangare na kasar nan.
Ya kara da cewa, wadanda suke son dole sai sun yi bikin binne gawar suna iya dakatar da yin haka har zuwa lokacin da za a shawo kan cutar ta Ebola, sai su fito da gawar su sake yi mata jana’iza irin wadda suke so.
Ya bayar da misali da abin da ya faru a cikin al’ummarsa lokacin yana makarantar sakandare inda aka yi sakaci wajen kula da wani wanda cutar kwalara ta kama shi, daga bisani cutar ta kusan cinye daukacin al’ummar yankin.
Shugaban ya ce, “Na tattauna da mutane da dama a ciki da wajen kasar nan tun lokacin da cutar Ebola ta bulla, kuma a tattaunawar da na yi da babbar darektar hukumar lafiya ta Majalisar dinkin Duniya (WHO) Misis Maget Chan, ta ce daga binciken da suka gudanar, kashi 60 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar Ebola sun samu cutar ne a lokacin da suke rufe gawa.”
“Shi ya sanya da wannan babbar darektar ta hukumar WHO ta yi mini wannan bayanin na ga ya kamata mu shawarci mutane su dakatar da bikin binne gawa. Saboda haka muna kira ga shugabannin addini da su dakatar da mafi yawan abubuwan da suke yi a yayin binne gawa, mu rika sauraron shawarwarin masana harkar kiwon lafiya domin mu tsirar da mutanenmu.’’
Jonathan ya bayyana cewa, “Idan muka yi abin da ya kamata game da cutar Ebola, za mu iya shawo kan matsalar a cikin watanni biyu, sai mu cigaba da gudanar da rayuwarmu yadda muka saba.’’
Shi ma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci musulmi, a wata sanarwa da Sakataren Jama’atu Nasril Islam, Dokta Khalid Aliyu ya sanya wa hannu, cewa su rika kaffa-kaffa a yayin da suke jana’iza kuma su kula da tsabtar muhallinsu da masallatansu, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Jami’in baki na kungiyar ECOWAS, wanda shi ma ya kamu da cutar a sakamakon cudanya da ya yi da marigayi Mista Patrick Sawyer lokacin da ya shigo kasar nan a ranar 20 ga watan Yuli, ya rasu ranar Talata, wanda ya sanya ya zama mutum na uku da ya rasu a Najeriya a sakamakon kamuwa da cutar, sauran biyun su ne, Mista Patrick Sawyer da kuma wata jami’ar jinya.
A halin yanzu dai an rufe ofishin ECOWAS da ke Legas, a yayin da kuma aka sanya ma’aikatan ofishin a cikin mutane 170 da ake lura da su saboda cudanya da suka yi da Mista Sawyer.
Kilishi ba ya haifar da Ebola –Dokta Nasir Gwarzo
Daga Abubakar Ibrahim, a Legas
Sabanin jita-jitar da ake yayatawa cewa wai ana iya samun cutar Ebola daga cin nama Kilishi, shugaban yaki da wannan cutar na kasa, Dokta Nasir Sani Gwarzo ya ce wannan batu babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin ba a samun wannan cutar ta dabbobin gida ko kuma a nama dafaffe ko gasasshe.
Ya ce ko a dabbobin dajin ma sai a wadansu daidaiku ne ake samu, kuma su ma sai ta hanyar mu’amala da jininsu ko ruwan da ke jikinsu, amma batun cin kilishi a kamu da wannan cutar, wannan babu gaskiya cikinsa ko kadan.
Doktan ya shaida wa wakilinmu cewa mutane su saki jiki su ci kilishi domin babu cutar Ebola a cikinsa.
Ya ce tun daga ranar da gwamnatin tarayya ta fara yaki da wannan cutar, kullum sai ta tantance masu shigowa kasar kafin ta bar su, domin ko sai an yi wa mutum gwajin zafin jiki mai nasaba da cutar tukunna kafin a bar shi ya shigo.
Dokta Nasir ya ce ko a ranar Litinin, sai da aka yi wa mutane kusan 500 gwaji tsakanin bakin iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, haka kuma mutane 985 aka yi musu irin wannan gwajin a filin jirgin saman Nmamdi Azikwe da ke Abuja kafin a bari su shigo cikin Najeriya, kuma duka an yi sa’a babu wanda zafin jikinsa ya wuce abin da ake tsoro.
Sai dai ya ce ba duka bakin iyakokin ake wannan gwajin ba, domin har yanzu ba a samu wadatattun wadannan kayan awon ba, amma yana fata cikin wannan makon a samu wadatattun kayayyakin, kuma da zarar sun samu, hatta masu gittowa ta wadannan iyakokin da kafa su ma za a rika yi musu wannan gwajin.
Dokta Nasir ya ce biyar daga cikin mutane takwas da aka killace ana kula da su saboda kamuwa da cutar suna samun sauki kwarai da gaske, su ma sauran ukun ana fata su samu sauki nan ba da jimawa ba.
Likitan ya kuma shawarci masu kwankwadar ruwan gishiri da su daina, domin suna kara dagula harkokin kiwon lafiyarsu ne, saboda babu wani wurin da aka samo cewa shan ruwan gishiri yana maganin cutar Ebola. Wadanda kuma ba su bari ba, to su kwana da sanin cewa suna kara tura kansu cikin matsala ne.
Mutane sun cigaba da shan ruwan gishiri a Legas
Abubakar Haruna, Daga Legas da Husaini Isa, a Jos
Duk da kiraye-kirayen da likitoci suka rika yi da shawarar da Hukumar Lafiya ta Majalisar dinkin Duniya (WHO) ta bayar na mutane su guji yin amfani da ruwan gishiri don maganin cutar Ebola, binciken Aminiya ya gano cewa mazauna Jihar Legas sun ci gaba da sha tare da yin wanka da ruwan gishirin.
Mutane da dama da Aminiya ta tattauna da su a jihar sun bayyana cewa suna ci gaba da yin amfani da gishiri saboda imanin da suka yi cewa kariya ne daga cutar.
Malam Mustafa Sani cewa ya yi, “Gaskiya ban daina shan ruwan gishiri ba kuma ban daina wanka da shi ba. Saboda ni na yi imani kuma na yarda da wadanda suka fada mini cewa na rika wanka da shi Allah zai kare ni daga kamuwa daga cutar Ebola. Kuma ai shi da ma gishiri magani ne mutane ne ba su ankara ba tun tuni sai yanzu da suka ga haza”.
Malama Maimuna Muhammadu kuwa cewa ta yi, “Ni har yanzu ina wanka da shi saboda malamai ne suka fada mana suka ce mu karanta kulhuwallahu kafa 41 da kula’uzai a cikin ruwan mu sha kuma mu yi wanka. Saboda haka zan ci gaba da yin amfani da gishirin har sai malamanmu sun ce mu dakata”.
Shi ma Malam Sule Tanko cewa ya yi, “Ina ci gaba da yin wanka da gishiri, saboda na yarda kariya ne daga kamuwa daga cutar Ebola. Tunda na fara wanka da shi na samu natsuwa kuma na ji canji a jikina, duk da ba shi da dadin sha, amma duk da haka mu mun yarda yana magani”.
A kalla mutane sama 20 ne aka kwantar a asibitoci daban-daban na garin Jos, babban birnin Jihar Filato, a makon da ya gabata, sakamakon shan ruwan gishiri don rigakafin cutar Ebola.
Mutane da dama a jihar sun yi ta shan ruwan gishiri tare da yin wanka da shi a ranar Alhamis din makon da ya gabata.
Kwamishinan lafiya na Jihar Filato, Dokta Fom Dakwak, wanda babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar, Dokta Elias Pede ya wakilta, ya yi bayanin cewa ruwan gishiri ba shi da wata alaka da warkarwa ko riga-kafin cutar.