An fi kamuwa da cutar Ebola daga gawa – Hukumar WHO
Ruwan gishiri da namijin goro ba sa maganin cutar Ebola –Dokta Amina Wata fitacciyar likita a Jihar Legas, Dokta Amina Ahmed ta ce ruwan gishiri ko namijin goro ba su iya kare mutum daga kamuwa daga cutar Ebola.Dokta Amina, wacce ita ce babbar jami’ar lafiya a karamar Hukumar Apapa/Iganmu, ta yi furucin haka ne yayin […]
(FILES) A file handout picture taken and released on August 7, 2014 by the Spanish Defense Ministry shows Roman Catholic priest Miguel Pajares, who contracted the deadly Ebola virus, being transported from Madrid’s Torrejon air base to the Carlos III hospital upon his arrival in Spain. The Carlos III hospital confirmed the death of evacuated […]

Ruwan gishiri da namijin goro ba sa maganin cutar Ebola –Dokta Amina
Wata fitacciyar likita a Jihar Legas, Dokta Amina Ahmed ta ce ruwan gishiri ko namijin goro ba su iya kare mutum daga kamuwa daga cutar Ebola.
Dokta Amina, wacce ita ce babbar jami’ar lafiya a karamar Hukumar Apapa/Iganmu, ta yi furucin haka ne yayin da take tattaunawa da Aminiya ta waya a Yammacin ranar Litinin.
Ta ce, “Shan ruwan gishiri ko wanka da shi ko kuma cin namijin goro ba sa maganin cutar Ebola kuma ba sa zama rigakafi daga kamuwa daga cutar, don binciken kimiyya bai nuna haka ba. Hasali ma idan mutum yana da wani ciwo, kamar hawan jini, idan ya sha gishiri zai iya kara ciwon ko kuma ya tayar da shi. Idan ma ba ka da ciwon, shan ruwan gishiri zai iya kawo shi. Haka shi ma namijin goro ba ya maganin cutar. Saboda haka ya kamata mutane su kiyaye”.
Ta ci gaba da cewa, “Abin da mutane ya kamata su yi shi ne su rika yawaita wanke hannayensu, musamma ma idan sun shiga bayan gida (makewayi) da kuma bayan sun fito, sannan a rika yawan tsafta da wanke bayan gida. Kuma mutane su rika kula da zarar sun ga wani yana fama da zazzabi su kai shi asibiti cikin gaggawa”.
Ta yi kira ga jama’a su guji yada jita-jita kan abin da ya shafi kiwon lafiya, don yin hakan na iya jefa wadansu cikin hadari.
Musulmi su guji amfani da jita-jita –Sheikh Aliyu
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Wani malamin addinin Musulunci da ke Zariya, Sheikh Aliyu Abdullahi Taled ya jawo hankalin al’ummar musulmi da su kiyayi sauraron jita-jitar a da ake yadawa na yin wanka da ruwan gishiri tare da shan ruwan domin kauce wa kamuwa da cutar Ebola.
Ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a masallacin Juma’a da ke Tudun Jukun a karamar Hukumar Zariya.
Ya shawarci musulmi da su tsaya kan imaninsu kuma su yarda cewa Allah ne kadai Zai iya saukar musu da cuta Ya kuma saukar musu da maganin cutar. Sai kuma ya bukaci da a daina yada farfagandar da babu gaskiya a cikinta.
Ya bukaci musulmi su rika ambaton Allah a dukkan al’amuransu kuma su ji tsoran Allah tare da yawaita salati ga Manzon tsira Annabi Muhammadu (S.A.W) kuma da zarar an samu labarin bullar wata masifa su rika fadin “Innalillahi Wa inna Ilaihi raji’un”, Allah zai karba mana.
Jihar Yobe ta dauki mataki
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Ma’aikatar lafiya ta Jihar Yobe ta bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da jita-jitar da wadansu ke yadawa cewa wai an samu bullar Ebola a wani sashi na jihar, babu kamshin gaskiya a kan hakan.
Kwamishinan lafiya, Dokta Bello Kawuwa ne ya bayyana haka ga Aminiya da ta tuntube shi dangane wannan jita-jitar da ake yadawa.
Kwamshinan ya kara da cewa, ma’aikatarsa a shirye take ta fuskanci kowane irin kalubale dangane da wannan cuta ta Ebola a kowane irin mataki.
Dokta Kawuwa ya ba da tabbacin cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da wayar da kan jama’a domin sanin alamominta tare da ilmantar da su yadda za su kare kansu daga kamuwa da ita.
Ya gargadi masu tu’ammali da namun daji, musamman ma mutanen da ke farautar namun daji a matsayin sana’a da su yi hattara yayin da suke gudanar da wannan sana’a tasu, kasancewar akasarin wannan cuta an fi samunta ne a jikin dabbobin daji.
Ya kuma gargadi jama’a da su yi kaffa-kaffa da saukar da duk wani bako da ya taho daga kasashen da wannan cuta ta fi yaduwa don kauce wa shiga halin jangwam.