An fi sayen hula Aisha Buhari da Maja da ATM – Mai hula
Ahmad Kala mai hula Kaugama ya tattauna da wakilinmu kan sana’ar sayar da hula wadda ke da dadadden tarihi a kasar Hausa, sai dai ana samun sauyin zamani, inda a yanzu sana’ar ke bin huluna na zamani, wanda manyan masu kudi da ’yan siyasa kan saya su rika sanyawa, wadanda suka fi fice irin su […]

Ahmad Kala mai hula Kaugama ya tattauna da wakilinmu kan sana’ar sayar da hula wadda ke da dadadden tarihi a kasar Hausa, sai dai ana samun sauyin zamani, inda a yanzu sana’ar ke bin huluna na zamani, wanda manyan masu kudi da ’yan siyasa kan saya su rika sanyawa, wadanda suka fi fice irin su ya bayyana irin nau’in huluna da suka fi yin fice da suka hada da Aisha Buhari da ATM da kuma Buhari ya dawo da Maja. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminniya: Yaushe ka fara wannan sana’a ?
Ahmad Kala: Ban dade da fara wannan sana’a ba, domin a bara na shigeta, sai dai na kai kamar shekara 30 ina dinkin hula
Aminiya: Kana nufin dinkin hula ka fara matsayin sana’a daga bisani kuma ka koma sayar da huluna?
Ahmad Kala: Eh! dinkin na fara daga baya kuma na dawo ina sayarwa kamar yadda ka sameni ina dinka wannan ta hannuna.
Aminiya: Ko za ka fada mana irin hulunan da kuma sunayensu?
Ahmad Kala: To na farko dai akwai wata hula da matasa suke sanyawa da kuma mutane masoyan Muhammad Buhari shugaban kasa, saboda haka ne ma aka sanya mata suna Aisha Buhari, kuma akwai Buhari ya-dawo da Maja da ATM. To wadannan su aka fi saye wadannan sune huluna da akafi so aka kuma fi saye .
Aminiya: Hular da ka ce sunanta ATM me ya sa aka sanya mata suna haka?
Ahmad Kala: To abin da yasa aka sanya mata suna haka yawanci ma’aikatan banki ne suka fi sayenta suna sanyawa.
Aminiya: Ko mene ne bambancin dinkin hula lokacin ada da kuma yanzu ?
Ahmad kala: Tunda ka yi min wannan tambaya ina yi wa Allah godiya saboda a da can matasan mu sai su rika sayen kayan da za su rika matse su, amma yanzu sun gane sayen hulunan da za su yi adon mutuncinsu da kimarsu ta fita a yanzu matashi sai ya caba ado yana alfahari ya shiga gari da martaba ta Bahaushe da ma kuma da ita aka san shi.
Aminiya: A huluna da ka ambata a baya wadanne ne suka fi tsada,kuma wacce a cikin su aka fi saye ?
Ahmad Kala: To gaskiya dai kam Aisha Buharin nan ita aka fi saye, ita ce hular da idan za ka yi yawo a kullum sai an tambaye ka ita ga mu masu sayarwa in dai kana da ita ta sayarwa ka fita sai an tambayeka ita a saya. Domin idan takwai 10 kana da ita cikin ’yan kwanaki za ka sayar da ita.
Aminiya: Akalla farashinta zai kai Naira nawa?
Ahmad Kala: To farashinta ya tashi daga Naira dubu hudu zuwa dubu 3,500 zuwa abin da ya kama, amma kuma akwai bambancin zare wanda kamar wannan da ka ganni ina dinkawa zan iya sayar da ita ma Naira dubu 15.ma zuwa 20.
Aminiya: Wane kalubale yawanci mutane ’yan kasuwa irinku suke fuskanta a sana’ar nan ?
Ahmad Kala: Gaskiya kalubalen da nake fuskanta shi ne na rashin jari
Aminiya: Sakonka ga matasa da kuma sauran masu hali na raina sana’a suna yawon maula?
Ahmad Kala: Zan yi amfani da wannan dama in yi kira ga matasanmu gaba daya. Abu na farko mutum ya dogara da kansa ko da mahaifin mutum yana da hali ka tashi ka nemi naka. Abu na biyu kuwa ina kira ga matasa ’yan uwana, musamman wadanda suka zo bariki da su guji watsar da iyalinsu suna mancewa da su, ba zuwa ba aike, su yi ta bushasha suna bugewa ga matan banza.