An fille kan yaro ɗan shekara 14 a Ibadan
Ana zargin abokansa ne suka sare mas kai domin yin tsarin kuɗi
Wasu da ake zargin matsafa ne sun fille kan wani yaro ɗan shekara 14 domin yin tsafin kuɗi a garin Ibadan, Jihar Oyo.
An fille kan Malik Kareem ɗan shekara 14 ne a unguwar Olorisaoko da ke Ƙaramar Hukumar Akinyele a ranar Asabar.
Shaidu sun bayyana cewa ya gamu da ƙarar kwana ne bayan rubuta jarrabawarsa ta kammala makarantar sakandare a kwanan baya.
Wani ɗan uwansa ya ce saurayin da da abokansa uku sun je wurin wani boka a ranar Asabar, inda suka nemi ya yi musu tsafin kuɗi.
- Rogo ya yi ajalin magidanci da iyalinsa su bakwai a Sakkwato
- An sace N50bn daga asusun Gwamnatin Kano —Muhyi
- ’Yan bindiga sun harbe matafiya 7 a hanyar Taraba
Majiyar ta ce, wanda aka kashe din ba a sani ba, ashe sauran yaran sun riga sun shirya da bokan cewar za su kashe shi don yin tsafin kudin.
“Ina gida wani ƙanina ya zo ya sanar da ni abin da ya faru, muka garzaya wurin domin mu tabbatar da hakan.
“Ko da muka isa wurin, bokan ya riga ya tsere, amma mun tarar da gawar ɗan uwanmu a kasa babu kai.
“A kwance cikin jini muka samu a gawar a gidan, an riga an ƙona kan.
“Sauran yara ukun ne a baya suka shirya da bokan cewa za su yi amfani da abokinsu wajen yin tsafin kuɗin.
“Don haka da suka isa wurin sai suka shake shi har ya mutu, aka sare masa kai, aka kuma ƙona.
“Ana zargin za su yi amfani da shi don shan kunu kowace rana,” in ji shi
Wani daga ’yan uwan mamacin ya ce, “Wasu matasa a yankin sun ƙona gidan bokan,” bayan aukuwar lamarin, kamar yadda jaridar Punch ruwaito.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya ce tuni suka, “fara bincike kan lamarin, kuma za a sanar da ku inda aka kwana.”