An fitar da jadawalin gasar rukunin Premier na Ingila
A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin gasar rukuni-rukuni na Ingila da ake wa lakabi da Premier League. Ana sa ran za a fara gasar ce a ranar Asabar 17 ga watan Agusta mai zuwa. Mai rike da kofin watau Manchester United za ta yi tattaki […]
A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin gasar rukuni-rukuni na Ingila da ake wa lakabi da Premier League.
Ana sa ran za a fara gasar ce a ranar Asabar 17 ga watan Agusta mai zuwa.
Mai rike da kofin watau Manchester United za ta yi tattaki ne gidan kulob din Swansea a wasan farko.  Sunderland za ta hadu da Fulham yayin da West Brom kuma za ta hadu da na Southampton sannan West Ham ta kece raini da na Cardiff.