An fitar da jerin sunayen mawakan da suka fi kudi a duniya
Mujallar Forbes mai bayani kan hamshakan masu kudi ta fitar da jerin sunayen mawakan da suka fi kudi a duniya.Ta fitar da jerin sunayen ne a makon jiya inda mawaki P. Diddy yake matsayi na daya inda ya mallaki Naira biliyan 8 da miliyan 880 (Dala miliyan 50), sai Jay Z da ya mallaki biliyan […]
Sean P. Diddy Combs arriving to the 2004 CFDA Awards at the New York Public Library in New York City on June 7, 2004. Manhattan, New York Photo © Matt Baron/BEImages

Mujallar Forbes mai bayani kan hamshakan masu kudi ta fitar da jerin sunayen mawakan da suka fi kudi a duniya.
Ta fitar da jerin sunayen ne a makon jiya inda mawaki P. Diddy yake matsayi na daya inda ya mallaki Naira biliyan 8 da miliyan 880 (Dala miliyan 50), sai Jay Z da ya mallaki biliyan 6.6 (Dala miliyan 43), sai Dr. Dre da ya mallaki Dala miliyan 40, sai Nicki Minaj da Naira biliyan 4.6 (Dala miliyan 29), sai Birdman da Naira biliyan 3.3 daidai da Dala miliyan 21, sai Kanye West da Naira biliyan 3.2 daidai da Dala miliyan 20, sai Lil Wayne da Dala miliyan 16, sai Wiz Khalifa da Dala miliyan 14.
Sauran sun hada da Ludacris Dala miliyan 12, sai Pitbull da Dala miliyan 11, sai Drake da Dala miliyan 10.5, sai Snoop Lion da Dala miliyan 10.