An ga dan Saurauniyar Ingila yana tallar mujalla a kan titi

Yarima William yana sayar da mujalla kwana hudu bayan kammala bikin cikar mahaifiyarsa shekara 70 a kan mulki

An ga dan Saurauniyar Ingila yana tallar mujalla a kan titi

Daga hannun dama, Yarima William dan Sarauniyar Ingila Elizabeth II dake sayar da mujalla tare da wani abokin aikinsa. (Hoto: anewa.com.tr)

An ga Yarima Mai Jiran Gado na Birtaniya, William, yana tallan wata mujalla a kan titunan birnin Landan.

Mazauna birnin Landan sun yi kicibus da Yarima William mai shekara 39 ne a lokacin da yake daga kwalin tallar mujallar The Big Issue, a yankin Westminster na birnin a ranar Alhamis.

Wani mai suna Richard Hannant, mai shekara 47, ya tura hoton da surukinsa mai suna Mathew Gardner ya dauka a tare da yariman yana sayar da mujallar.

A tare da hoton da Richard ya wallafa a shafinsa na Linkedin, Mathew Gardner ya ce, “Na samu babbar alfarma ta yin gaba-da-gaba da sarki mai jiran gado a yayin da yake aiki ta karkashin kasa domin taimakon marasa galihu.”

Sai Richard ya mayar da martani da cewa, “Abin da ya fi burgewa shi ne Yarima William ya tambayi surukina (Mathew) ko zai sayi ‘The Big Issue,” shi kuma ya ce: ‘Ai ba ni da canji’. 

“Nan take William ya fito da na’urar biyan kudi ta tafi-da-gidanka. Ba ka da mafita.”

Shi ma wani direban tasi a birnin Landan, Neil Kramer, ya wallafa hotonsa a dandalin sada zumunta tare da Yarima Williman yana sayar da mujalla.

Hakan ta faru ne kwana hudu bayan kammala bukuwan cikar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, shekara 70 a kan karagar mulki.

An ga Yarima William, wanda shi ne Duke din Cambridge kuma magajin Sarauniya Elizabeth II, sanye da hula hana-sallah, yana daga kwalin yana kiran mutanen da ke wucewa a kan hanya su zo sayi mujallar da yake talla.

The Big Issue mujalla ce da ta mayar da hankali wajen kawo rahotanni kan mutane da marasa gidaje da masu kwana a kan tituna a kasar Birtaniya.

William ya dade yana fafutikar ganin yadda za a magance matsalar rashin muhalli da masu kwana a kan tituna a kasar ta Birtaniya.

Shi ne kuma Uban kungiyar jinkai ta Centrepoint, wadda ke yaki da matsalar tun a shekarar 2005.

A watan Disamban 2009, shi da shugaban kungiyar sun kwana a kan titi a yunkurinsu na gano hakikanin halin da marasa muhalli suke ciki.

William shi ne kusan mafi shahara a cikin ’ya’yan Sarauniya Elizabeth II, kuma ana ganin shi a matsayin mai saukin kai da kuma taimakon marasa galihu.