An ga wata a Najeriya —Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan ranar Alhamis. Sarkin Musulmin ya ce an samu labarin ganin watan ne daga shugabannin addini da kungiyoyi daban-daban a Nijeriya. Hakan dai na nufin Juma’a 24 ga watan Afrilu 2020 […]
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ba da sanarwar ganin watan Ramadan ranar Alhamis.
Sarkin Musulmin ya ce an samu labarin ganin watan ne daga shugabannin addini da kungiyoyi daban-daban a Nijeriya.
Hakan dai na nufin Juma’a 24 ga watan Afrilu 2020 ta zama 1 ga watan Ramadan 1441.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya roki Musulmi su yaiwata addu’a a cikin wannan watan Allah Ya kawo karshen annobar coronavirus.
“Ina kira ga mutane su bi umarnin da jami’an lafiya da gwamnatoci suka sanya kan kare kamuwa da cutar coronaviru”, inji shi.
Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga masu wadata su taimaki talakawa a watan Ramadana ba tare da kula da bambancin siyasa da kabila ba.
Sai dai kuma bai zayyano garuruwan da aka ga watan ba, amma ya ce kwamitin ganin wata ya tantance sahihancin duk bayanan da aka samu kafin a kawo maganar gaban shi.