An ga watan Ramadan a Najeriya

Sarkin Musulmi wanda ya sanar da ganin watan a garuruwan Maiduguri da Bama da ke Jihar Borno, ya buƙaci al’ummar Musulmin Najeriya da su tashi da azumin Ramadan a ranar Asabar 1 ga watan Maris, 2025

An ga watan Ramadan a Najeriya

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya.

Sarkin Musulmi ya buƙaci al’ummar Musulmin Najeriya da su tashi da azumi a ranar Asabar, 1 ga watan Maris 2025, zuwa ƙarshen watan, mai kwanaki 29 zuwa 30.

Da yake sanar da ganin watan a fadarsa da ke Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa an tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a garuruwan Bama da Maiduguri da ke Jihar Borno da ma wasu wurare.

Don haka, Asabar 1 ga watan Ramadan 1446 Bayan Hijira, ta yi daidai da 1 ga watan Maris 2025 Miladiyya.

Sanarwar tasa ta zo ne ’ sa’o’i bayan hukumomin ƙasar Saudiyya sun tabbatar da ganin watan a Ƙasa Mai Tsarki.

Sarkin Musulmi ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.

Ya roki mutane su yi wa kasa da shugabanni a addu’a domin samun ɗorewar zaman lafiyaa Najeriya.

Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn

Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano

An ga watan Ramadan a Najeriya

Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki