An ga watan Ramadan a Saudiyya

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Saudiyya, ta tabbatar da cewa gobe Laraba ce ɗaya ga watan Ramadan.

An ga watan Ramadan a Saudiyya

Mahukunta sun sanar da ganin jinjirin watan Ramadan yammacin wannan Talatar a ƙasar Saudiyya kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Saudiyya, ta tabbatar da cewa gobe Laraba ce ɗaya ga watan Ramadan na 1447 Hijiriyya.

Tuni dai hukumomi a Najeriya suka buƙaci musulman ƙasar da su nemi jinjirin watan a yau Talata, 17 ga Fabrairu 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1447AH.

Buƙatar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

Sanarwar ta buƙaci Musulmi su fara neman jinjirin watan azumi a wannan rana, tare da umartar duk wanda ya ga watan da ya kai rahoto ga shugaban ƙaramar hukuma ko Dagaci mafi kusa domin a isar da saƙon ga Fadar Sarkin Musulmi.