An ga watan Zhul-Hijjah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Hakan na nufin ranar Laraba, 28 ga watan Yuni za a yi Babbar Sallar bana

An ga watan Zhul-Hijjah a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da Litinin, 19 ga watan Yunin 2023, a matsayin 1 ga watan Zhul-Hijjah a Najeriya, sakamakon ganin jinjirin watan a ranar Lahadi.

Hakan dai na nufin ranar Laraba, 28 ga watan Yuni ce za ta kasance ranar Babbar Sallah a Najeriya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin ganin watan ya fitar da yammacin Lahadi,

Sanarwar ta ce, “Fadar mai alfarma Sarkin Musulmai ta ayyana Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023 a matsayin 1 ga watan Zhul-Hijjah, 1444, bayan Hijira. Hakan na nufin a bana za a yi Idin Babbar Sallah ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023 a matsayin ranar Babbar Sallah.

“Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, yana taya dukkan al’ummar Musulmai barka da Sallah,” in ji Sarkin na Musulmi, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA).

Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja

MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP

Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas

Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo