An gabatar da Sallar Rokon Ruwa a Saudiyya

An gabatar da addu’ar rokon ruwa a ranar Alhamis a birnin Makkah da ke kasar Saudiyya kamar yadda yake a koyarwar Annabi Muhammad (SAW). Imam Shaikh Abdullah Awad Al-Juhani ne ya jagoranci rokon ruwan a Masallacin Haramin kuma Yarima Khalid Al-Faisal Dan Sarkin Saudiyya na daga cikin mahalarta. Matsalar tsaro: Yadda fasinjoji suka kauracewa hanyar […]

An gabatar da Sallar Rokon Ruwa a Saudiyya

Massalacin Makkah

An gabatar da addu’ar rokon ruwa a ranar Alhamis a birnin Makkah da ke kasar Saudiyya kamar yadda yake a koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

Masallacin Haramin Makkah a lokacin addu’ar rokon ruwa.

Imam Shaikh Abdullah Awad Al-Juhani ne ya jagoranci rokon ruwan a Masallacin Haramin kuma Yarima Khalid Al-Faisal Dan Sarkin Saudiyya na daga cikin mahalarta.

Imam Sheikh Abdulbari Al-Thubaity shi ya jagoranci gabatar da sallar rokon ruwan a Massalacin Annabi Muhammad (S.A.W.) dake garin Marina, inda Yarima Saud bin Khalid Al-Faisal, Mataimakin Gwamnan Madinah ya halarci sallar.

An kuma gabatar da addu’ar rokon ruwan a sauran yankunan kasar ta Saudiyya da suka hada da Najran, Qassim, Jaran da Gabashin Asir kamar yadda yake a Sunna.