An gano abin fashewa da ake zargin makamin Amurka ne a Neja
Ana zargin abin fashewar wani yanki ne na makami mai linzami da Amurka ta harba a Najeriya a kwanakin baya.
Jama’a sun shiga firgici bayan da aka gano wani abu da ake zargin abin fashewa a yankin Zugurma da ke Karamar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.
Ana zargin abin fashewar da aka gano wani yanki ne na makami mai linzami kirar Tomahawk da Amurka ta harba a Najeriya a kwanakin baya.
Wasu mazauna yankin ne suka hango abin fashewar a cikin daji sa’annan suka sanar da jami’an tsaro domin kawo dauki.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Njea, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cewa an gano abin fashewar kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kai.
- Kwana 25 ke nan ban ji muryarsa ba — Matar Khalifa Sani Zaria
- Yara 469 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Kano
- Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin rataye matar da ta kashe tsohon mijinta
A cewarsa: “A ranar Litinin 5 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 2 na rana, rahoto ya iso daga yankin Zugurma na Karamar Hukumar Mashegu cewa wasu mazauna sun hango wani abu da ake zargin makami ne a cikin daji.
“Jami’an ‘yan sanda na Ibbi Div sun isa wurin, suka kewaye tare da tsare makamin, sannan aka tura rundunar EOD-CBRN ta jihar domin gudanar da bincike, tantancewa da kuma kwashe abin. Ana gunadar da bincike a kan abin, kuma za a sanar da sakamakon bincinken a nan gaba.”