An gano asusun banki 593 da Emefiele ya boye kudade a kasashen waje

Babban Mai Binciken CBN ya gano asusun bankunan kasashen waje 593 da tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele ya ɓoye kudade

An gano asusun banki 593 da Emefiele ya boye kudade a kasashen waje

Godwin Emefiele

Babban Mai Binciken Babban Bankin Najeriya (CBN) da Shugaba Bola Tinubu ya nada ya zargi tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele, da bude asusun ajiya guda 593 ta bayan fage a kasashen waje.

Rahoton da mai binciken ya mika wa Shugaba Tinubu ya nuna Emefiele ya yi gaban kansa ne wajen bude asusun ajiyar kasashen wajen, ba tare da amincewar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kwamitin gudanarwan CBN ba.

Takardun binciken da wakilinmu ya gani sun nuna nuna cewa Emifiele ya bude asusun ne bankuna daban-daban a kasashen Birtaniya, Amurka da kuma China.

Duk da cewa ba a bayyana sakamakon binciken a hukumance ba, amma majiya mai tushe a fadar shugaban kasa ta tabbatar wa wakilinmu cewa an mika wa Shugaba Tinubu rahoton a ranar Laraba, 20 ga watan nan na Disamba, 2023.

A ranar 9 ga watan Yunin 2023 ne Tinubu ya dakatar da Emefiele, kuma tun daga jami’an tsaro ke tsare da shi.

A ranar 30 ga watan Yuli Tinubu ya nada babban jami’in hukumar bayar da rahoton kudi ta Najeriya, Jim Obazee, a matsayin mai bincike na musamman na CBN.

A wasikar nadin, Tinubu ya bukaci Obazee ya binciki CBN da kuma manyan cibiyoyin kasuwanci na gwamnati, kuma “wannan nadin zai kasance tare da aiki nan take kuma ka mika rahoto ga ofishina kai tsaye.”

Takardun da wakilinmu ya gani a ranar Alhamis sun nuna cewa kawo yanzu rahotanni biyu aka mika wa Tinubu, kuma na karshen cikinsu shi ne na ranar 20 ga watan Disamba, da ke bayyana laifukan da ake tuhumar Emefiele da sauran su.

Rahoton ya kuma bukaci a gurfanar da wasu manyan jami’an CBN da suka yi aiki da Emefiele, da kuma wasu daga wajen CBN, bisa zargin wasu laifuka daban-daban.

Bude Asusun kasar waje ba bisa ka’ida ba

Daya daga cikin takardun da wakilinmu ya gani ya nuna cea Emefiele ya zuba kudin gwamnatin Najeriya a wasu asusu 593 na kasashen waje ba tare da izini ba.

Rahoton ya ce “Mai binciken ya yi nasarar gano ɗaukacin asusun da aka sanya biliyoyin kudaden.

“A Burtaniya kadai, Emefiele ya ajiye kudi fam 543, 482,213, ba tare da izini daga hukumar CBN da kwamitin zuba jari na bankin ba.

“Mai binciken yana ba da shawarar a gurfanar Emefiele saboda ajiye kudadaen ba bisa ka’ida ba, da kuma amfani da kudaden ba ta hanyar da ta dace ba.”

Rahoton ya kara da cewa an kuma bankado wasu biliyoyin Dalar Amurka da Yuan na China a asusun da Emefiele ya bude ta bayan fage.

Kafin binciken na baya-bayan nan, a watan Yuli, an gurfanar da Emefiele bisa tuhume-tuhume biyu na mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, wanda kotu ta bayar da belin sa a kan Naira miliyan 20.

A 2022, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta zarge shi da tallafa wa ta’addanci da dai sauransu.

Wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa sun fito fili ne a daidai lokacin da ake zargin sa da shiga siyasa da neman takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC a zaben 2023.

A ranar 17 ga watan Nuwamba, Babbar Kotun Birnin Tarayya ta tsare Emefiele a Gidan Yari na Kuje bisa zargin laifin zamba.

Tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta tuhume shi da laifuka 20 masu alaka da zambar kwangila ta Naira biliyan 6.5, amma daga baya aka rage su zuwa shida da kudi N1bn kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Emifiele dai ta bakin lauyoyinsa, ya musanta zargin da ake yi masa.

Sauran laifukan da ake zargin Emefiele

Aminiya ta ruwaito cewar daga sabon binciken da aka mika wa Shugaba Tinubu rahoto a ranar Laraba, akwai yiwuwar an bankado wasu sabbin batutuwa zargin da gwamnati ke wa Emefiele.

Sauran laifuffukan Emefiele da mai binciken ya ce ya kamata a gurfanar da Emefiele a a kai sun hada da sake fasalin kudi wanda binciken ya nuna ya jefa ’yan Najeriya da tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.

Sauran sun hada da Naira biliyan 1.7 da aka kashe a matsayin kudaden shari’ar buga kudin, tallafin COVID-19 N1.622trn; da sauransu.

Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura