An gano boyayyun gwal-gwalai da suka shekara 900 a tukunya
Masu binciken ma’adanai sun gano wasu boyayyun gwala-gwalai da suke da yakinin an boye su ne shekara 900 da suka gabata a birnin Caesarea da ke kasar Isra’ila. An gano ma’adanan ne tare da wani dan kunnen gwal a cikin tukunyar tagulla a tsakanin wasu duwatsu da ke gefen bango. Tukunyar tagullar da aka saka […]
Masu binciken ma’adanai sun gano wasu boyayyun gwala-gwalai da suke da yakinin an boye su ne shekara 900 da suka gabata a birnin Caesarea da ke kasar Isra’ila.
An gano ma’adanan ne tare da wani dan kunnen gwal a cikin tukunyar tagulla a tsakanin wasu duwatsu da ke gefen bango.
Tukunyar tagullar da aka saka gwala-gwalan ta kasance, kamar asusun ajiya ga wanda ya boye da nufin wata rana zai zo ya dauki ajiyarsa, amma daga bisani bai dawo ba har tsawon shekarun.
A cewar masu binciken ma’adanan, ganin shekarun gwala-gwalan wanda ya mallake su ya riga ya rasu, tun wani harin kisan gilla da sojojin Crusader a shekarar 1101 suka kai birnin.
Wannan bincike da aka gudanar ya shahara wajen gano abin da jama’ar karni na 11 suka mallaka a wani shirin binciken ma’adanai da aka gudanar a birnin Caesarea da ake yi a duniya.
Masu binciken sun ce sun gano gwala-gwalan a tsakanin wasu duwatsu biyu da ke gefen wani gida da suke makwabtaka tun a zkarni na 11.
Wannan binciken da aka gano ya shiga cikin tarihi a birnin Caesarea tun bayan juyin mulkin sojojin Crusaders suka yi. Kamar yadda hukumomin kasar Isra’ila suka sanar.
Rahotanni sun ce, sojojin Baldwin I, wanda ya jagoranci masarautar Jerusalem a shekarar 1100 da 1118 sun kashe mafi yawan mazauna birnin Caesarea,.
Daraktocin binciken ma’adanan D0kta Peter Gendelman da Mohammed Hatar, sun fahimci cewa wadanda suka mallaki gwala-gwalan an kashe su ne yayin da aka mai da wadansu bayi don haka ba su samu damar dawowa kan gwala-gwalansu ba.
Binciken da aka gudanar na kusa, shi ne wanda aka gano tukunyar gwal da sarkar tagulla a 1960 da kuma tarin tagulla a 1990. Wadannan na kusa da aka gano an ajiye su a gidan tarihi na Jerusalem a kasar Isra’ila.
A shekarar 2015 masu bincike a karkashin ruwa sun gano gwala-gwalai a gabar tekun Isra’ila wanda ya kai kusan dubu 2 da aka kiyasta sun kai shekara dubu 1 a karkashin ruwa kamar yadda masu binciken ruwan suka sanar.