An gano Daliban Kankara a dajin Zamfara
Gwamna da sojoji sun musanta ikirarin Boko Haram na garkuwa da daliban GSSS Kankara
Gwamnan Katsina, Aminu Masari, ya ce sun samu kwararan bayanai cewa daliban makarantar GSSS Kankara da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su na tsare a Jihar Zamfara.
Gwamna ya ce bayanai sun nuna cewa masu garkuwar na rike da yaran a cikin daji a Jihar Zamfara, “kuma ko ba dukkansu ba to mafi rinjayensu dai suna can wajen.”
- Daliban GSSS Kankara da aka sace suna raye — DHQ
- An bude iyakokin Najeriya, amma banda shigo da shinkara
- Nan da watan Janairu Najeriya za ta shigo da rigakafin COVID-19 —Minista
“A yanzu haka jami’an tsaro sun zagaye dukkan wadannan wurare da ake zaton yaran suna can”, inji gwamnan.
Ya ce a halin yanzu gwamnati na kokarin karbo yaran amma ba da karfin bindiga ba, don kauce wa tsautsayin da ke iya kaiwa ga jikkata yaran ko kashe su.
“Amma ba ma so a yi harbi ta sama ko ta kasa saboda kada wasu daga cikinsu ta shafe su; muna bin duk hanyoyin da suka kamata na tabbatar da cewa an amso yaran cikin lafiyarsu ba tare da an rasa rai ba, ko an ji wa wani rauni ba”, inji shi.
‘Karya Boko Haram take yi’
Ya musanta ikirarin kungiyar Boko Haram na yin garkuwa da daliban, inda ya ce a iya saninsu, masu garkuwa da mutane ne suka dauke su kuma da su ake tattaunawa.
“Su muka sani, kuma su ne muke da yakinin cewa da su ake ta batun tattaunawar nan.
“Maganar ’yan Boko Haram idan maganar da ake yi da su ta kai ga sun gwada cewa akwai wasu daga waje to a lokacin ne tunanin cewa Boko Haram na da hannu na kai tsaye zai zo.
“Amma mun sani an bayar da rahoto cewa Boko Haram na da alaka da wasu ’yan ta’addan nan,” a kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana hakan ne wata hira a Sashen Hausa na BBC ya yi da shi a daren Alhamis.
Bayanin gwamnan na zuwa ne daidai ranar da Rundunar Tsaro ta Najeriya ta karyta ikirarin Boko Haram na yin garkuwa da daliban na GSSS Kankara.
Kakakin Rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya yi fatali da ikirarin ne a lokacin da yake cewa rundunar na tsaka da aikin ceto daliban.
Ya ce ikirarin Shugaban Boko Haram, Ibrahin Shekau cewa daliban na GSSS Kankara na hannunsu farfaganda ce da kungiyar ta saba yi.
Ya kara da cewa bayanan da rundunar ta samu sun nuna yaran na a raye kuma babu wani abin da ya same su; babban abin da hukumomin tsaro suka sa a gaba shi ne ceto su ba tare da wata illa ba.
“Babu wanda ya mutu, babu wani rahoto da muka samu daga binciken da muke yi da ya nuna cewa akwai wanda ya mutu, kuma sojoji na kan aiki.
“Sun fara sintiri a yankin, sai dai ba zan bayyana ba yanzu domin tattabar da babu yaron da ya salwanta an kuma ceto su da ransu,” inji Kakakin na Rundunar Tsaro.
A jawabin nasa na ranar Laraba, Enenche ya nesanta Rundunar Tsaron da hannu a tattaunawa da ko biyan masu garkuwar fansa.
Ya ce, amma idan gwamnan ya ga tattauna batun fansa da masu garkuwar shi ne mafi a’ala a gare shi, to yana da ikon yin haka a matsayinsa na uba a jiharsa.