An gano ganda mai guba a kasuwannin Jihar Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta gargadi mutanen jihar bisa wata ganda mai guba da aka gano a kasuwannin jihar.Kwamishiniyar noman jihar, Ronke Sokefun ta shaida cewa ganin yadda kasuwancin ganda ke garawa a kasuwannin jihar sai wasu baragurbin ’yan kasuwa suka fara fasakwabrin fatar jima da ake jeme ta da sinadarai masu guba. Ta ce: “’Yan […]

An gano ganda mai guba a kasuwannin Jihar Ogun
An gano ganda mai guba a kasuwannin Jihar Ogun

Gwamnatin Jihar Ogun ta gargadi mutanen jihar bisa wata ganda mai guba da aka gano a kasuwannin jihar.
Kwamishiniyar noman jihar, Ronke Sokefun ta shaida cewa ganin yadda kasuwancin ganda ke garawa a kasuwannin jihar sai wasu baragurbin ’yan kasuwa suka fara fasakwabrin fatar jima da ake jeme ta da sinadarai masu guba. Ta ce: “’Yan kasuwar suna shigowa da jemammiyar fatar ne daga kasashen Turai da Japan da Italy da Sudan, fatun da ake sarrafa su domin yin takalma da jakukkuna, sai ga shi an kawo don a sayar a ci a kasuwannin Jihar Ogun. Hakan ya sa gwmnatin jihar ta yi hadin gwiwa da hukumar kula da kayan abinci da magunguna ta NAFDAC domin zakulo baragurbin ’yan kasuwar. Sun kuma yi kashedi bisa illar gandar mai guba, za kuma a iya gane ta domin launinta baki-baki ne kuma tana da kauri sossai da wari na musamman,” inji ta.
Binciken Aminiya ya gano cewa al’umma a kurmi suna matukar son cin ganda, wacce suka fi kira da ‘Kfomo.’ Sukan yi farfesunta ko su sanya ta a miya a cikin abinci.