An gano gawar basarake bayan ya shekara 2 a hannun ’yan bindiga
’Yan sanda da ke aiki a yankin Bori a Jihar Ribas sun gano gawar Basaraken lardin Luwa a Jihar Ribas, Cud Robert Loolo, wanda aka yi garkuwa da shi. Tun a shekarar 2019 ’yan bindiga suka yi garkuwa da basaraken a fadarsa da ke Karamar Hukumar Khana ta Jihar ta Ribas. ’Yan kwallon Najeriya 3 […]
’Yan sanda da ke aiki a yankin Bori a Jihar Ribas sun gano gawar Basaraken lardin Luwa a Jihar Ribas, Cud Robert Loolo, wanda aka yi garkuwa da shi.
Tun a shekarar 2019 ’yan bindiga suka yi garkuwa da basaraken a fadarsa da ke Karamar Hukumar Khana ta Jihar ta Ribas.
- ’Yan kwallon Najeriya 3 da ke daukar sama da miliyan 30 a sati
- Jami’an tsaro sun cafke malamin ’yan bindiga a Kaduna
DPO na yankin Bori, SP Bako Angbashim ne ya jagoranci ’yan sandan da suka shiga cikin duhun dajin da suka gano gawar basaraken mai shekara 61 a dajin da ke tsakanin garuwan Bera da Bani inda masu garkuwa da shi suka kashe shi bayan sun karbi kudin fansarsa sau biyu.
Ya ce a ranar Litinin da ta gaba ce aka gano gawar basaraken ta riga ta rube a wurin da ’yan bindigar suka daure shi har ya mutu.
Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen da ke addabar yankin Ogoni za su fuskanci fushin hukumar ’yan sanda.
Daya daga cikin ’ya’yan basaraken mai suna Doka Douglas Fabeke ya nuna takaicinsa bisa yadda ’yan bindigar suka yi wa mahaifinsu kisan gilla bayan sun karbi kudin fansa har a karo na biyu, inda ya nuna godiyarsa ga Allah bisa gano gawar mahaifin nasu.
Ya ce har gida wasu guggun matasa da ke rigima a kan shugabanci suka iske mahaifin nasu suka sace.
“Jami’an tsaro da sauran jama’ar gari sun yi kokarin shiga tsakani inda lamarin ya kai ga mun ba su kudin fansa har sau biyu amma abin ya ci tura.
“Daga baya an yi nasarar kame wani boka wanda ya shaida mana cewa an kashe mahaifin namu, amma bai san inda aka binne shi ba.
“Sai yanzu da Allah Ya ba mu nasara muka gano gawar kuma ga duk alamu sun azabtar da shi kafin su kashe shi,” Inji shi.
Zuwa yanzu dai an kai gawar basaraken dakin ajiyar gawa kafin daga bisani a yi masa sutura.